GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 70 duk da Hamas ta amince ta saki fursunoninta da ke hannunta
Wannan ya biyo bayan kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Isra'ila a ranar Juma'a da ta "daina kai hare-hare a Gaza nan take" bayan Hamas ta bayyana shirin sakin fursunonin Isra'ila a ƙarƙashin shirin tsagaita wuta da Trump ɗin ya gabatar.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 70 duk da Hamas ta amince ta saki fursunoninta da ke hannunta
Trump ya bayyana shirinsa mai matakai 20 a ranar 29 ga Satumba, wanda ya haɗa da sakin fursunonin Isra'ila cikin awanni 72 / AA
5 Oktoba 2025

Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 70, ciki har da mata da yara a hare-haren jiragen sama da take kai wa a Gaza da ta yi wa ƙawanya, duk da ikirarin rage hare-haren kan fararen-hula, in ji Hamas.

"Wannan ci gaba da zubar da jini yana bayyana ƙaryar ikirarin gwamnatin Netanyahu mai laifukan yaƙi game da rage hare-haren soji kan fararen-hula marasa kariya," in ji ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu a wata sanarwa a ranar Asabar.

Ta yi kira ga al'ummar duniya, ƙasashen Larabawa da Musulmi, da su amfani da doka ta jin kai ta hanyar kare Falasɗinawa, bayar da agaji, da kuma ƙara matsa lamba don kawo ƙarshen "yaƙin halakarwa" da yunwa da aka kwashe shekaru biyu ana yi a Gaza.

Wata sanarwa daga Ofishin Watsa Labarai na Gaza ta ce sojojin Isra'ila sun kai hare-haren jiragen sama har 93, inda suka kashe mutane 70, ciki har da 47 a birnin Gaza.

Wannan ya biyo bayan kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Isra'ila a ranar Juma'a da ta "daina kai hare-hare a Gaza nan take" bayan Hamas ta bayyana shirin sakin fursunonin Isra'ila a ƙarƙashin shirin tsagaita wuta da ya gabatar, yana mai cewa yana ganin ƙungiyar tana "shirye don zaman lafiya mai ɗorewa."

Masar ta sanar a ranar Asabar cewa za ta karɓi wakilan Isra'ila da Hamas a ranar Litinin don tattauna cikakkun bayanai game da musayar fursunoni a matsayin wani ɓangare na shirin Trump na kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

Trump ya bayyana shirin sa mai matakai 20 a ranar 29 ga Satumba, wanda ya haɗa da sakin fursunonin Isra'ila cikin awanni 72 bayan amincewar Isra'ila, tsagaita wuta, da kuma ƙwace makaman Hamas.

Kisan ƙare-dangi na Isra'ila

Tel Aviv ta ƙiyasta cewa akwai fursunoni 48 na Isra'ila da ke Gaza, ciki har da 20 da ke raye.

A gefe guda, Isra'ila tana tsare da kimanin fursunoni 11,100 na Falasɗinu, da dama daga cikinsu suna fuskantar azaba, yunwa, da kuma rashin kulawar lafiya, a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam na Falasɗinu da Isra'ila.

Isra'ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 67,000, mafi yawansu mata da yara, a cikin wannan ta'addancin da take yi a Gaza da ta yi wa ƙawanya

Ta rusa mafi yawan yankin, ta kuma tilasta wa kusan dukkan mazauna yankin barin gidajensu.