GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Abubuwan da muka sani game da martanin Hamas kan shirin Trump a Gaza
Hamas ta amince ta saki dukkan Isra'ilawa da ke hannunta, waɗanda suke a raye da waɗanda suka mutu, a ƙarƙashin shawarwarin shugaban Amurka Trump game da Gaza sannan ta ce a shirye take ta shiga yarjejeniyar tsagaita wuta nan-take.
Abubuwan da muka sani game da martanin Hamas kan shirin Trump a Gaza
Hamas izražava "zahvalnost" za arapske, islamske i međunarodne posredničke napore, uključujući one koje predvodi Trump. / TRT World
14 awanni baya

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas da ke Falasɗinu ta mayar da martani a hukumance game da daftarin shawarwari na shugaban Amurka Donald Trump game da yankin Gaza.

Wakilan ƙasashen Qatar da na Falasɗinu sun bayyana cewa Hamas ta nemi ƙarin haske game da wasu saɗarori da ke cikin ƙudurin amma ta ƙara da cewa a shirye take ta shiga tattaunawar tsagaita wuta ta hannun masu shiga tsakani.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta amince ta saki dukkan Isra'ilawa da ke hannunta, waɗanda suke a raye da waɗanda suka mutu, kamar yadda Trump ya bayar da shawara.

Sai dai wani babban jami’in Hamas ya shaida wa Al Jazeera cewa miƙa mutanen cikin awanni 72, kamar yadda aka bayar da shawara, abu ne "da ba zai yiwu ba".

Hamas ta jaddada amincewarta ta miƙa harkokin gudanarwa na Gaza ga wata hukuma ta ƙwararru ta Falasɗinawa, inda ta ƙara da cewa dole ne duk wani shiri game da makomar Gaza ya kasance cikin “babban tsari na ci-gaban ƙasar” wanda zai ƙunshi dukkan ɓangarorin Falasɗinu da ba sa ga maciji da juna sannan a gina shi bisa dokokin ƙasashen duniya.

Hamas ta miƙa "godiya" ga Larabawa da ƙasashen Musulmai da sauran ƙasashen duniya game da ƙoƙarinsu na tabbatar da tsagaita wuta, ciki har wanda Trump ya jagoranta.

Hamas ta ja hankali game da wata saɗara a cikin ƙudurin na Trump da ke magana game da “makomar Zirin Gaza da kuma ‘yancin al’ummar Falasɗinu" tana mai cewa kamata ya yi "dukkan ‘yan ƙasa da kuma dokokin ƙasashen duniya" su kasance waɗanda za su samar da makomar yankin.