Abubuwan da muka sani game da samamen zalunci da Isra’ila ta kai wa Ayarin jiragen Global Sumud
GABAS TA TSAKIYA
7 minti karatu
Abubuwan da muka sani game da samamen zalunci da Isra’ila ta kai wa Ayarin jiragen Global SumudTare da kashe Falasdinawa sama da 66,000 da Isra’ila yi tun 7 ga Oktoban 2023 da jefa Gaza cikin yunwa, jiragen ruwa na Global Sumud Flotilla sun dauki kayan tallafi masu muhimmanci kuma masu fafutuka na bijirewa mamayar.
'Yan kasashe da dama ne suka hau jiragen ruwa don zuwa Gaza da nufin karya kawanyar Isra'ila / AP
4 awanni baya

Sojojin ruwa na Isra'ila sun kai hari kan Ayarin Jiragen Ruwa na Duniya, Global Sumud Flotilla, na aikin jinƙai na lumana da ya kunshi jiragen ruwan fararen-hula kusan 50 da kuma mahalarta sama da 500, da suka hada da masu fafutuka, 'yan majalisa, da 'yan jarida daga kasashe daban-daban.

Jiragen ruwa masu dauke da kayan agaji da magunguna, sun kama hanyar zuwa Gaza a karshen watan Agusta.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru da irin wannan adadin jiragen ruwa suka yi tafiya tare zuwa Gaza, dauke da fararen hula 532 da suka fito daga kasashe sama da 45.

Isra'ila ta ci gaba da yin kawanya ga Gaza mai mutane kusan miliyan 2.4 kusan shekaru 18, sannan ta kara tsaurara matakan tsaro a watan Maris lokacin da ta rufe mashigar kan iyaka da kuma hana kai kayan abinci da magunguna, lamarin da ya jefa yankin cikin yunwa.

Tun daga watan Oktoban 2023, harin bam da Isra'ila ta kai ya kashe Falasdinawa sama da 66,000, mafi yawan su mata da yara kanana.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha yin gargadin cewa an mayar da yankin yanayin ba za a iya sama a cikin sa ba, inda yunwa da cututtuka ke yaduwa cikin sauri.

Ta yaya Isra’ila ta mayar da martani?

Sojojin ruwan Isra'ila sun shiga cikin jiragen ruwa tare da tsare masu fafutuka da dama, amma sa'o'i 12 bayan da sojoji suka fara katse jiragen ruwa, wasu jiragen sun ci gaba da tafiya kuma suna kusa da yankin da aka yi wa kawanya a ranar Alhamis.

A cewar masu bibiyar motsin jiragen ruwan Flotilla, ya zuwa yanzu sojojin Isra'ila sun tsare akalla masu fafutuka 317 daga cikin jiragen ruwa 21, ciki har da 'yan kasar Turkiyya 25.

Ana jigilar masu fafutukar zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashdod ta Isra'ila, inda za a fitar da su zuwa Turai, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila.

Ayarin jiragen ruwan na Global Sumud Flotilla na bayyana motsinsu ta yanar gizo ta kyamarori kai tsaye a cikin kwale-kwale daban-daban, ko da yake an samu katsewar hanyoyin sadarwar da dama yayin da hukumomin Isra'ila suka fara kutsa wa ruwan kasa da kasa a yammacin Laraba.

Na'urar bin diddigin jirgin ta nuna cewa akalla jiragen ruwa 20 ne aka katse yayin da wasu ke tafiya kuma da alama na da nisan mil kadan daga Gaza, kuma jirgin ruwa daya da alama ya tsallaka zuwa yankin Gaza, a cewar masu fafutukar.

Sadarwa kai tsaye, an katse sadarwa

Daga cikin masu fafutuka da sojojin Isra'ila suka tsare har da Greta Thunberg, tsohuwar magajin garin Barcelona Ada Colau, 'yar majalisar Turai Rima Hassan da sauransu.

Jiragen ruwan na da nisan mil 70 daga Gaza a lokacin da aka kama su, a cikin wani yanki da Isra'ila ke aiki don dakatar da duk wani jirgin ruwa da ke zuwa yankin.

Masu shirya tafiyar sun ce an lalata hanyoyin sadarwarsu da suka hada da amfani da na’urar daukar hoto kai tsaye daga wasu jiragen ruwa.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila ta fitar da hotuna da bidiyo na masu fafutuka, tana mai cewa a cikin wata sanarwa ta X suna nan "kalau kuma a cikin koshin lafiya".

Tun da farko, watsa abubuwan da ke faruwa kai tsaye da daddare daga masu fafutuka, ya nuna jiragen ruwan Isra'ila na tunkarar jiragen ruwansu, suna fesa musu ruwa da fitulu masu haske kafin sojoji su shiga cikin jiragen.

Da suke tsammanin za a tsare su, masu fafutuka sanye da rigunan ruwa don ceton rai sun zauna cikin da'ira tare da ɗaga hannayensu sama.

Wasu sun yi nasarar yada wannan lokacin kai tsaye daga wayoyin su kafin su jefa na'urorinsu cikin teku.

Me duniya ke cewa? 

Wannan katsalandan dai ya haifar da tofin Allah tsine.

Magoya bayan jirgin sun fito kan tituna a biranen Turai da dama - da suka hada da Rome, Naples, Barcelona da Athens - don yin Allah wadai da ayyukan Isra'ila da hare-haren da Isra'ilan ke ci gaba da kai wa.

Babbar kungiyar kwadago ta Italiya ta yi kira da a gudanar da yajin aikin gama-gari na kwana daya a ranar Juma'a, wanda ake sa ran zai toshe dukkanin manyan bangarorin da suka hada da sufuri da makarantu.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausar suka ga harin da sojojin ruwan Isra'ila suka kai, tana mai bayyana shi a matsayin "aikin ta'addanci" da kuma keta dokokin kasa da kasa, in ji wata sanarwa da ta fitar a yammacin Laraba.

‘Fashi a kan teku’

Ma'aikatar ta ce tana kokarin ganin an sako 'yan kasar Turkiyya da sauran masu fafutuka da sojojin Isra'ila ke tsare da su cikin gaggawa.

Shugaban Colombia Gustavo Petro ya bayar da umarnin korar dukkan tawagar diflomasiyya ta Isra'ila sakamakon tsare wasu 'yan Colombia biyu a cikin jirgin ruwa tare da kawo karshen yarjejeniyar kasuwanci marar shinge ta Colombia da Isra'ila.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta bayyana goyon bayanta ga masu fafutuka sannan ta kira kutsen Isra'ila kan jiragen ruwan a matsayin "laifi", inda ta yi kira ga jama'a da su yi zanga-zangar yin Allah wadai da Isra'ila.

Kungiyar Jihad Islama ta Falasdinu ta kira harin da "fashin teku", inda ta dora alhakin tsirar mutanen kan Isra’ila.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman ya bayyana matakin na Isra'ila a matsayin haramun kuma ya soki hadin kan kasashen yamma ke ba wa kasar.

Shan alwashin kare ‘yan kasa

Turai ta bukaci Isra'ila da ta mutunta dokokin kasa da kasa da kuma kare masu fafutuka, indda shugabanni ke yin gargadi game da matsalolin jin kai a yankin.

Shugabannin kasashen Asiya da suka hada da Pakistan, Malaysia, da Maldives, sun yi kakkausar suka ga harin tare da sha alwashin kare 'yan kasashensu.

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya kira harin na dabbanci, yayin da Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya yi gargadin cewa kasarsa za ta dauki dukkan matakan shari'a don tuhumar Tel Aviv.

Me dokar kasa da kasa kan amfani a teku ta ce?

Dokokin kasa da kasa na amfani da teku gabaɗaya sun taƙaita ikon kasashe zuwa mil 12 na ruwan teku, amma duk da haka Isra'ila na da'awar tana da hujjar aika soji a ƙarƙashin dokokin da suka shafi rikici.

Masana haƙƙin ɗan adam suna cewa ofisoshin ayyukan jin kai sun kare haƙƙin wuce wa ta yankin.

Yuval Shany, kwararre kan dokokin kasa da kasa a jami'ar Hebrew ta yammacin birnin Kudus, ya ce muddin dai killace Gazan da Isra'ila ta yi ya zama "mai hujjar jibge sojoji" - da nufin kawar da makamai - kuma jirgin da ke da nufin karya kawanyar, to Isra'ila za ta iya kutsa wa cikin jirgin bayan bayar da gargadin farko.

Ko wannan kawanyarr ta dace tare da kawo sojoji, ko kuma ba ta dace ba batu ne da ake ta muhawara a kai.

Wannan ayari na jiragen ruwa na wakiltar mafi yawan ayyukan farar hula don kalubalantar killace Gaza na shekaru 18 da Isra'ila ta yi.

Wannan lamarin ya yi kama da harin Mavi Marmara na 2010, inda sojojin Isra'ila suka kashe 'yan gwagwarmayar Turkiyya tara tare da raunata wasu da dama a cikin wani jirgin ruwan agaji da ke kan hanyarsa ta zuwa Gaza, lamarin da ya haifar da rikicin diflomasiyya mai tsanani tsakanin Turkiyya da Isra'ila.

Masu lura da al'amuran yau da kullun sun yi gargadin cewa harin na baya-bayan nan na da nasaba da sake haifar da tashe-tashen hankula, yayin da kuma ke nuna yadda Isra'ila ke ci gaba da mamaye wa da toshe hanyoyin shiga zirin Gaza, wanda kungiyoyin kare hakkin dan’adam da na Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana a matsayin hukuncin bai daya da ya sabawa doka a karkashin dokokin kasa da kasa.