Rundunar sojan Isra'ila ta fara janye sojojinta daga Gaza zuwa wuraren da aka ƙayyade a cikin shirin Shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yaiƙn da ake yi a yankin na Falasdinawa da aka killace, kamar yadda kafofin watsa labarai na Isra'ila suka ruwaito.
“A cikin sa'o'i 24 masu zuwa, sojojin Isra'ila za su kammala janyewarsu daga wasu yankuna a cikin Gaza zuwa wajen da aka ambata “layin rawaya,” kamar yadda aka amince a cikin shirin Trump tsakanin Isra'ila da Hamas,” in ji tashar talabijin ta Isra'ila Channel 12 a ranar Juma’a.
Ta kara da cewa: “Ana sa ran sojojin za su janye zuwa gabas daga Rafah da Khan Younis (kudu) da kuma daga wasu yankuna a arewacin Gaza, suna kusantar iyakar Isra'ila.”
Da safiyar Alhamis, Trump ya sanar da cewa Isra'ila da ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas sun cim ma matsaya kan mataki na farko na shirin tsagaita wuta da musayar fursunoni.
Wannan yarjejeniya ta biyo bayan kwanaki hudu na tattaunawar kai-tsaye tsakanin anɓgarorin biyu a birnin Sharm el-Sheikh na Masar, tare da halartar wakilai daga Turkiyya, da Masar da Qatar, karkashin sa idon Amurka.