GABAS TA TSAKIYA
5 minti karatu
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta Trump
Yarjejeniyar da Amurka da Turkiyya da Qatar da Masar suka taimaka wajen ƙulla ta da kuma ba da tabbaci a kanta ita ce ƙoƙari na farko mai tsari da aka yi na dakatar da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza da a aka yi wa ƙawanya.
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta Trump
Dakarun Isra’ila suna tafiya kusa da kan iyakar Gaza, kamar yadda aka ɗauka daga kudancin Isra’ila, ranar Alhamis, ranar 9 ga watan Oktoba, 2025 / AP
17 awanni baya

Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza kashi na farko lamarin da zai sa Isra’ila ta yi musayar ɗaruruwan fursunoni Falasɗinawa domin ita ma a saki mutanenta da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Kazalika yarjejeniyar za ta sa Isra’ila ta janye dakarunta daga Zirin Gaza tare da bai wa ɗaruruwan motocin kayayyakin agaji damar shigar da kayan agaji yankin na Gaza.

Amincewar da majalisar ministocin ta yi da safiyar ranar Jumma’a ta biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla tsakanin Isra’ila da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas wadda ta fara aiki ranar Alhamis.

"Gwamnatin Isra’ila, a ƙarƙashin jagorancin Benjamin Netanyahu, ta amince da yarjejeniyar ta kawo ƙarshen yaƙi a Zirin Gaza da kuma dawo da dukkan fursunoni (fursunonin Isra’ila a Gaza)," kamar yadda wata sanarwar Isra’ila ta bayyana.

An fara zaman majalisar ministocin ne da jawabin tsaro daga babban hafsan sojin ƙasar Eyal Zamir, in ji rahotannin daga ƙasar, suna masu ƙarawa da cewa wakilin shugaba Trump na musamman a Gabas Ta Tsakiya, Steve Witkoff, da kuma surukin Trump', Jared Kushner, sun gana da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bayan sun gama tattaunawa.

Zaman ya biyo bayan jinkiri na sa’o’i bayan an kammala wata tattaunawa kan tsaro ta majalisar ministocin ba tare da kaɗa ƙuri’a kan yarjejeniyar Trump mai ƙudurori 20 ba.

Kafar watsa labarai ta Isra’ila KAN ta wallafa wata takarda mai taken "Cikakaken [shirin] kawo ƙarshen yaƙin Gaza",  tana mai cewa gwamnatin ta amince da yarjejeniyar, amma ministoci masu tsattsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich da Yitzhak Wasserlauf da kuma Amichai Eliyahu sun ƙada ƙuri’ar ƙin amincewa da shirin Trump.

 'Mun kawo ƙarshen yaƙi a Gaza'

An yi shelar yarjejeniyar tsagaita wutar ne da safiyar ranar Alhamis bayan an shafe kwanaki huɗu ana tattaunawa a kaikaice tsakanin Hamas da Isra’ila a birnin Sharm el-Sheikh na Masar da ke bakin Bahar Rum inda Turkiyya da Masar da Qatar da Amurka suka shiga tsakani. 

Zango na biyu na shirin ya yi kira da a samu wata sabuwar hanyar kafa gwamnati a Gaza ba tare da saka hannun Hamas ba, da kafa dakarun tsaro da suka ƙunshi Falasɗinawa da kuma dakaru daga ƙasashen Larabawa da Musulmai da kuma karɓe makamai daga hannun Hamas.

Ƙasashen Larabawa da Musulmai sun yi maraba da shirin.

Isra’ila da Hamas sun tabbatar da bin zango na farko na yarjejeniyar, wanda ya dogara kan ginshiƙai uku: musayar fursunoni da ficewar dakarun Isra’ila daga zuwa wasu yankuna da aka keɓe da kuma shigar da muhimman kayayyakin agaji cikin Gaza bayan shekaru da aka yi na hana su shiga.

Hamas ta ce musaya ta farko za ta sa a saki fursunonin Isra’ila 20 kuma za a saki fursunonin Falasɗinu 2,000.

Wannan ya haɗa da Falasɗinawa 250 da aka yi wa ɗaurin rai da rai da kuma 1,700, waɗanda yawancinsu mata ne da ƙananan yara, waɗanda aka kama tun lokacin da aka fara yaƙin. Ana tsammanin a yi musayar cikin sa’o’i 72 na fara aiwatar da yarjejeniyar.

Shirin mai ƙudurori 20, wanda ka fara bayyana shi ranar 29 ga watan Satumba, ya haɗa da musayar fursunoni ‘yan Isra’ila da fursunoni Falasɗinawa da tsagaita wuta da kuma miƙa makamai na Hamas da kuma sake gina Gaza.

Tun da farko ranar Alhamis, Trump ya bayyana cewa Amurka da sauran masu shiga tsakani sun taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila a Gaza, yana mai jaddada cewa ya kamata a saki ‘yan Isra’ila ranar Litinin ko Talata  kuma yana sa ran halartar liyafar rattaba hannu kan yarjejeniyar a Masar.

Ya ce, "Mun kawo ƙarshen yaƙi a Gaza," yana mai ƙarawa da cewa matakin zai kawo "zaman lafiya mai ɗorewa."

Babban mai sansatawa na Hamas, Khalil al Hayya, ya ce ƙungiyar ta gwagwarmayar Falasɗinawa ta samu tabbaci daga Amurka da masu shiga tsakani Larabawa da Turkiyya cewa kisan ƙare-dangin Isra’ila a Gaza zai zo ƙarshe gaba ɗaya.

Sai dai kuma, ministan tsaron ƙasa na Isra’ila mai ra’ayin riƙau Itamar Ben-Gvir ya yi gargaɗi ranar Alhamis cewa jam’iyyarsa mai tsattsarurar ra’ayi ta Jewish Power za ta ƙwace mulki daga gwamnatin Firaminista Netanyahu muddin ba a kawar da Hamas ba.

Tawagar sojin Amurka za ta ‘sa ido’ kan sulhun

Kazalika , za a tura wata tawagar sojojin Amurka ta dakaru 200 Gabas Ta Tsakiya domin "sa ido" kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza, kamar yadda manyan jami’an sojin Amurka suka bayya ranar Alhamis.

Adimiral Brad Cooper, shugaban rundunar sojin Amurka da ke Gabas Ta Tsakiya da kudancin Asiya ya ce, "daga farko za mu girke dakaru 200 a ƙasa.

“Aikinsu zai kasance na sanya ido , da kuma tabbatar da cewa ba a keta yarjejeniyar ba," kamar yadda wani babban jami’i ya shaida wa manema labarai.

Jami’an sojin Masar da Qatar da Turkiyya da kuma mai yiwau jami’an sojin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za su kasance a tawagar , in ji shi. 

Wani jami’i ya ce "babu sojin Amurka da ake son ya shiga cikin Gaza."