AFIRKA
3 minti karatu
Shugaban Kamaru Biya ya yi fitowar ba-zata, ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe
A baya bayan nan ba a ganin Shugaban Paul Biya a wajen yaƙin neman zaɓe, kasancewar bai jima da dawowa daga Switzerland ba, inda ya shafe kwanaki dama.
Shugaban Kamaru Biya ya yi fitowar ba-zata, ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe
Cameroon's President Paul Biya, who is seeking an eighth term, speaks while he stands next to his wife Chantal Biya during the rally in Maroua. / Reuters
9 awanni baya

Shugaban Kamaru mai shekaru 92, Paul Biya, ya gudanar da taron yaƙin neman zaɓensa na farko a ranar Talata a yankin Arewa Mai Nisa, wanda ke fama da rikice-rikice, yayin da shugaban ƙasar mafi tsufa a duniya ke neman tsawaita mulkinsa na shekaru 43 a zaɓen shugaban ƙasa da za a yi ranar 12 ga Oktoba.

Da yake jawabi ga taron magoya bayansa a filin wasa da ke garin Maroua, Biya ya yi alkawarin ƙara tsaro a yankin da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda, da rage matsalar rashin aikin yi ga matasa, da inganta tituna da kayan more rayuwa idan aka sake zaɓen sa a karo na takwas.

“Na san matsalolin da ke damun ku sosai, kuma na san abubuwan da ba a yi muku ba waɗanda ke sa ku shakku game da abin da zai faru gaba,” in ji shi a jawabin nasa. “Duba da ƙwarewata, zan iya tabbatar muku cewa waɗannan matsalolin ba su da wahalar warwarewa.”

Yankin Arewa Mai Nisa na Kamaru, wanda ke fama da hare-hare da sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa daga ƙungiyar Boko Haram, na ƙunshe da kusan kashi 20% na masu zaɓe miliyan 8.2 da ke da damar kada ƙuri'a a ƙasar.

Yawan tafiye-tafiye zuwa Turai

Tsofaffin abokan Biya kuma 'yan takarar adawa biyu daga cikin tara da ke neman shugabancin ƙasar — Bello Bouba Maigari da Issa Tchiroma Bakary — suna da magoya baya sosai a wannan yanki da Musulmai suka fi yawa, wanda kuma shi ne ɗaya daga cikin yankunan da suka fi talauci a Kamaru.

Wannan ne karon farko da Biya ya halarci yaƙin neman zaɓe saboda ba ya ƙasar, kasnacewar bai jima da dawowa daga wata ziyara da ya kai Switzerland ba.

Ba a bayar da wani dalili a hukumace kan wannan tafiya tasa ba, amma shugaban na Kamaru ya saba yin tafiye-tafiye zuwa Turai don hutu na kashin kai da kuma jinya a 'yan shekarun nan. Ba kasafai ake ganin Biya a bainar jama'a ba.

A cewar kiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya, akalla kashi 43% na al'ummar ƙasar na rayuwa cikin talauci, bisa ma'aunin kimar kuɗin shiga, da ilimi, da kiwon lafiya.

Rashin haɗin kan abokan hamayya

Duk da haka, ana ganin Biya zai iya samun nasara a kan sauran 'yan takarar a zaɓen ranar 12 ga Oktoba, musamman bayan da aka hana babban abokin hamayyarsa, Maurice Kamto, tsayawa takara a watan Agusta, kuma 'yan adawa sun kasa haɗa kai.

An cire iyaka wa'adin shugabancin ƙasa zuwa karo biyu ta hanyar kaɗa ƙuri’a a majalisa a shekarar 2008.