AFIRKA
2 minti karatu
Maroko ta rattaba hannu kan yarjejeniyar yaƙi da cin hanci bayan jerin zanga-zanga a faɗin ƙasar
An sanya hannu kan yarjejeniyoyin ne domin ƙarfafa samar da haɗin kai tsakanin muhimman hukumomi bayan jerin zanga-zangar da matasa suka jagoranta ta neman tsage gaskiya da gyara lamura a ƙasar Maroko.
Maroko ta rattaba hannu kan yarjejeniyar yaƙi da cin hanci bayan jerin zanga-zanga a faɗin ƙasar
Maroko ta rattaɓa hannu kan yarjejeniya ta yaƙi da cin hanci bayan jerin zanga-zangar da aka yi a fadin ƙasar / Reuters
12 awanni baya

Hukumomi a Maroko sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin ƙarfafa matakan hanawa da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa bayan jerin zanga-zangar da matasa suka jagoranta inda suka nemi a yi gyara kan harkokin gwamnati tare da tsage gaskiya.

Wata sanarwar gwamnati ta ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar INPPLC ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da hukumar tsaro ta DGSN da kuma hukumar shige da fice ta DGST.

An sanya hannu kan yarjejeniyoyin ne domin ƙarfafa samar da haɗin kai tsakanin muhimman hukumomi bayan jerin zanga-zangar da matasa suka jagoranta ta neman tsage gaskiya da gyara lamura a ƙasar.

Kazalika yarjejeniyar za ta samar da wani gurbi na bayar da horo na musamman ga hukumomi domin samar da ƙwarewa da kuma ƙarfafa ƙarfin gwamnati wajen tunkarar haɗuran cin hanci da rashawa.

Gwamnatin ta ce yarjejeniyar ta “nuna jajircewar Maroko wajen ƙarfafa hukumominta na cikin gida wajen yaƙi da cin hanci da rashawa ta wani tsari na haɗaka.”

Matakin yana zuwa ne bayan zanga-zanga a faɗin ƙasar da matasan da ake kira “Generation Z 212” suka shirya, wadda ta yi kira da yi gyara a fannin ilimi da lafiya da yaƙi da cin hanci da rashawa. Matasan sun dakatar da jerin zanga-zangar har zuwa ranar 9 ga watan Oktoba.