SIYASA
3 minti karatu
Shugaban Madagascar na ɓuya a wani 'wuri mai aminci' bayan mummunar zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar
"Tun daga ranar 25 ga watan Satumba aka yi yunkurin kashe ni da kuma yin juyin mulki'' a cewar shugaban na Madagascar.
Shugaban Madagascar na ɓuya a wani 'wuri mai aminci' bayan mummunar zanga-zangar da ta ɓarke a ƙasar
Shugaban ƙasar Madagascar Andry Rajoelina ya tsere daga ƙasar bayan mummunar zanga-zanga da ta barke / AFP
14 Oktoba 2025

Shugaban ƙasar Madagascar ya fada a ranar Litinin cewa ya tsere zuwa wani ‘wuri mai aminci’ bayan ‘‘kokarin hallaka shi da aka yi.”

Andry Rajoelina ya ce kunɗin tsarin mulkin ƙasar ne kaɗai zai iya warware wannan takun-saka da aka shafe makonni ana zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a kai .

‘‘An tilasta min tserewa zuwa wani “wuri mai aminci don kare rayuwata a yau” a cewar shugaban mai shekaru 51 a wani bidiyon kai-tsaye da aka yada ta shafin Facebook, ba tare da bayyana inda yake ba.

"Tun daga ranar 25 ga watan Satumba aka yi yunkurin kashe ni da kuma yin juyin mulki. Wasu gungun sojoji da 'yan siyasa ne suka shirya kashe ni," in ji shi.

A ƙarshe dai an soke jawabin ƙasa da Shugaba Rajoelina ya shirya yi bayan jinkirin da aka samu bayan da wata ƙungiyar daga rundunar sojin ƙasar ta yi koƙarin karɓe iko da kafafen yada labarai mallakin gwamnati.

Zargin fitar da shi

‘‘Tsarin mulkin ne kawai zai iya magance takaddamar,’’ in ji Rajoelina, wanda tun da farko aka ba da rahoton an fitar da da shi zuwa ƙasar Faransa a cikin wani jirgin soji ranar Lahadi bayan “yarjejeniya” da Shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Sai dai, a ranar Litinin Macron ya ki tabbatar da ko ƙasarsa wadda ta yi wa Madagascar mulkin mallaka ce ta fitar da shugaban yankin tsibirin da ke fama da rikici, yana mai shaida wa manema labarai a Masar cewa ‘‘ina mai bayyana damuwarmu matuka.’’

A shekarar 2009, Rajoelina ya haye kujerar mulkin Madagascar bayan juyin mulkin da ya haifar da bore da ya yi sanadiyar hambarar da tsohon shugaban ƙasar Marc Ravalomanana.

Tun daga ranar 25 ga watan Satumba ya ke fuskantar zanga-zangar da matasa ke jagoranta saboda tsananin rashin ruwa da wutar lantarki da kuma zargin almundahana da ya rikiɗe zuwa kiran ya yi murabus.

Rikicin dai ya janyo sauye-sauyen gwamnati da suka hada da rusa majalisar ministoci da naɗin sabon firaminista da shugabannin tsaro.

Sabon hafsan soji

Duk da haka, Rajoelina ya ci gaba da fuskantar turjiya a wurin sojoji daga Cibiyar Gudanar da ayyukan dakarun Soji (CAPSAT), wani rukunin sojoji da suka taimaka wajen hawan Rajoelina kan mulki ta hanyar juyin mulkin 2009, wadda ta bayyana goyon bayanta ga zanga-zangar.

A ranar Lahadi ne, CAPSAT ta nada sabon hafsan soji sa’o’i bayan da Rajoelina ya yi Allah-wadai da zanga-zangar da ta mara wa baya a matsayin yunkurin kwace mulki ba bisa ka’ida ba, kafin daga bisani abokansa, tsohon Firaminista Christian Ntsay da wani ɗan kasuwa Maminiaina Ravatomanga, suka tashi zuwa Mauritius a ranar Asabar.