Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da Afganistan
DUNIYA
5 minti karatu
Abin da muka sani game da mummunar arangamar kan iyaka tsakanin sojin Pakistan da AfganistanArangama cikin dare tsakanin dakarun Pakistan da Afganistan ta yi ajalin mutane da dama, hakan ya sanya aka rufe iyakokin kasashen biyu.
Arangama da tsakar dare tsakanin dakarun Pakistan da Afganistan ta janyo asarar rayuka da yawa.. / Reuters
6 awanni baya

Sojoji da dama ne aka kashe a rikicin da aka yi cikin dare tsakanin sojojin Pakistan da na Afganistan, in ji bangarorin biyu a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ke zama daya daga rikici mafi muni na kan iyaka tun bayan da kungiyar Taliban ta sake samun iko a watan Agustan 2021.

Rundunar sojin Pakistan ta sanar da cewa an kashe sojojinta 23 sannan wasu 29 sun jikkata.

A wata sanarwa da ta fitar, ta ce an kashe fiye da mambobin Taliban da masu alaka da su 200, tare da lalata wurare da dama na Taliban a kan iyaka da kuma sansanonin horar da mayakanta.

A yayin wani taron manema labarai a birnin Kabul, kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid ya ce an kashe sojojin Afganistan 9 da na Pakistan 58, yayin da wasu 30 suka jikkata.

Ya kara da cewa sama da ofisoshin tsaron Pakistan 20 ne dakarun Afganistan suka kwace na wani dan lokaci.

Me ya janyo arangamar?

Rikicin na baya bayan nan dai ya samo asali ne sakamakon yawaitar hare-haren da TTP ke kai wa sojojin Pakistan, ciki har da tayar da bama-bamai a arewa maso yammacin Pakistan.

Islamabad ta sha yin kira ga gwamnatin Taliban ta wucin gadi da ta jajirce wajen daukar mataki kan 'yan ta'adda na Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP), gamayyar kungiyoyin ta'addanci da dama.

'Yan ta'adda sun kashe jami'an tsaron Pakistan 11, ciki har da jami'ai biyu a ranar Talata, sannan kuma sun kashe wani jami'in sojan Pakistan a arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa a ranar Alhamis.

Pakistan ta ba wa 'yan ta'addar TTP lakabin "Fitna-al-Khawarij da Indiya ke daukar nauyi", yayin da "Fitna-al-Hindustan" kalma ce da aka sanya wa kungiyoyin ta'addanci da ke Balochistan.

Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Asif, ya yi ikirari a ranar Alhamis cewa gwamnatin wucin gadi ta Afganistan ta nemi kudi daga Islamabad don sauya matsugunin da 'yan ta'addar TTP daga kan iyakarta.

Kafafen watsa labaran kasar Pakistan sun bayyana cewa, Pakistan ta kai hari kan wasu 'yan ta'adda a cikin Afganistan a ranar Alhamis.

Da'awar da Pakistan ba ta musanta ba kuma ba ta amince da ita ba.

Pakistan ta yi zargin cewa gwamnatin Taliban ta bai wa 'yan ta'addar TTP damar gudanar da ayyukansu daga kasar Afganistan, yayin da Kabul ke musanta zargin tare da tabbatar da cewa ba su amince da kai hare-hare kan Pakistan daga yankinta ba.

Yankin Kashmir da ke karkashin ikon India

Pakistan ta kuma gabatar da babban korafi ga Afganistan kan sanarwar hadin gwiwa tsakanin India da Afganistan da aka fitar a ranar 10 ga Oktoba a New Delhi, tare da nuna matukar damuwa saboda da bayanai game da yankin Kashmir da India ke da iko da shi.

Ministan Harkokin Wajen Afganistan na rikon kwarya, Amir Khan Muttaqi, ya isa India don ziyarar diplomasiyya a ranar 9 ga watan Oktoba, karon farko da wani jami'in Taliban ya ziyarci New Delhi tun bayan da kungiyar ta dawo kan karagar mulki a shekarar 2021.

Pakistan ta aike da sammace ga jakadan Afganistan don isar da damuwar Islamabad.

Korafin ya ta'allaka ne kan batun Kashmir da Indiya ke da iko, a matsayin wani muhimmin yanki na India, wanda Pakistan ta ce cin zarafi ne kai tsaye ga kudurorin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) da kuma matsayin yankin da ake takaddama a kai.

Me dukkan bangarori biyun ke fada?

Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi Allah wadai da hare-haren na Afganistan, yana mai kiran su da " tsokana".

"Ba za a yi sulhu a kan tsaron Pakistan ba, kuma duk wata tsokana za ta fuskanci hukunci mai tasiri," in ji Sharif a cikin wata sanarwa, inda ya zargi mahukuntan Taliban a Afganistan da barin kasarsu ta yi amfani da 'yan ta'adda.

A halin da ake ciki, Afganistan ta kare yamutsin a matsayin "ayyukan ramuwar gayya," tare da bayyana cewa "An shawo kan dukkan iyakokin Afghanistan na karkashin cikakken iko".

Sake bullar rikici

An dawo da kai hare-haren ta'addanci a arewa maso yammacin Khyber Pakhtunkhwa tun bayan janyewar da Amurka ta yi da kuma komawar 'yan Taliban mulki, wanda mafi yawan hare-haren na kungiyar TTP ne.

A cewar jami'an sojin Pakistan, sama da mutane 500 ne suka mutu, ciki har da sojoji 311, a hare-haren da aka kai a bana.

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya lura da cewa TTP tana samun "tallafin kayan aiki" daga gwamnatin Taliban ta Kabul.

Tsohuwar jami'ar diflomasiyyar Pakistan Maleeha Lodhi ta ce tashe-tashen hankula a yankin kan iyaka "ya jefa dangantakar da ke tsakanin makwabta cikin koma baya" amma ta kara da cewa diflomasiyya na da matukar muhimmanci ga magance rikicin.

Ministan Tsaron Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa kokarin da ake yi na shawo kan kungiyar Taliban ta Afganistan ya ci tura.

Ya kara da cewa "Ya isa haka. Hakurin gwamnatin Pakistan da sojojin ya kare."

Rikicin ya sanya an rufe wasu muhimman hanyoyin kan iyaka guda biyu, Torkham da ke arewa maso yamma da Chaman-Spin Boldak a kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya dakatar da zirga-zirgar kasuwanci da farar hula a tsakanin kasashen, a cewar jami'an Afganistan.