Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta kama ma’aikatan jinƙai takwas bisa tuhumar leƙen asiri, inda ta zarge su da ɗaukan bayanai masu muhimmanci na ƙasar tare da bai wa ƙasashen waje.
Ma’aikatan su takwas na aiki da Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa Mai Zaman Kanta ta INSO, ƙungiyar da ke da cibiya a Holland kuma take bayar da taimakon jinƙai.
Ƙungiyar ta tattara tare da naɗar muhimman bayanai game da sojojin ƙasar ta Yammacin Afirka, ciki har da yankunan da ake kai farmakai, hanyoyin jerin gwanon motoci da yawan jami’an da ake kai wa, in ji Ministan Tsaro Mahamadou Sana, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata..
Daga cikin wadanda aka kama har da ‘yan ƙasar Faransa biyu, ciki har da daraktan INSO a Burkina Faso, da wani ɗan kasar Czech, da ɗan ƙasar Mali da ‘yan Burkina Faso huɗu, in ji Ministan.
Bai bayyana takamaiman yaushe ne aka yi kamen ba.
INSO ta bayyana a ranar Talata cewa suna tattara bayanai ne kawai don sanya ido kan tsaro da kare ma’aikatan agaji.
“Bayanan da muka tattara ba na sirri ba ne kuma waɗanda jama’a suka riga suka sani ne,” in ji kungiyar.
INSO ta kuma aƙra da cewa tana bayar da cikakken haɗin kai ga mahukuntan Burkina Faso a binciken da suke yi, kuma tana aiki don ganin an saki ma’aikatan nata da aka tsare.
Burkina Faso na yaƙi da ta’addanci da ya taɓarɓara al’amura a ƙasar ta Yammacin Afirka tsawon shekaru.