DUNIYA
2 minti karatu
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
Babban Alkalin kotun tarayya ya dakatar da shirin gwamnatin Trump na korar ma’aikatan Muryar Amurka sama da 500, yana mai zargin shugabannin hukumar da suka hada da Kari Lake da kin bin umarnin kotu kan tabbatar da dokokin aikin jarida na VOA.
Babban Alkalin Kotun Amurka ya dakatar da umarnin Trump na korar ma’aikatan VOA
Babban Alkalin kotun Amurka ya dakatar da umarnin korar ma'aikatan VOA / Reuters
9 awanni baya

 Wani babban alkalin kotun Tarayya da ke zama a birnin Washington, ya umarci gwamnatin Trump a ranar Litinin da ta dakatar da korar daruruwan ma'aikata daga hukumar USAGM da kafar yada labarai ta Muryar Amurka ke karkashinta, inda ya kara da cewa jami'an gwamnati sun nuna rashin mutunta umarnin kotun.

Babban Alkalin Royce Lamberth ya dakatar da shirin yayin da yake tantance ko Hukumar Kula da Kafafan Yada Labaran Duniya ta Amurka USAGM ta bi umarnin da ya bayar a watan Afrilu na cewa ‘‘ta cika wa’adin da doka ta yanke wa kafar VOA na kasancewa muryar da za a dogara a kanta wajen yada labarai a ko yaushe.’’

Matakin korar dai ya shafi ayyuka 532 na ma’aikatan da ke aiki a kafar, adadin da ke wakiltar mafi yawan sauran ma’aikatan hukumar.

A watan Maris ne dai aka rufe kafar watsa shirye-shiryen Muryar Amurka (VOA) ba zato ba tsammani karkashin umarnin Shugaban Ƙasar Donald Trump.

Masu AlakaTRT Afrika - Ma'aikatan gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) sun kai Trump ƙara kotu

A takardar umarnin da ya rubuta Lamberth ya bayyana cewa ‘‘ba shi da wani shakku’’ wadanda ake tuhuma da suka hada da hukumar da mukaddashin shugabanta Kari Lake, "ba su da wani shiri na bin umarnin farko na kotu".

A maimakon haka, "suna ta ɓata lokaci yayin da suke ci gaba da take hakki na mafi ƙarancin dokar da ta kafa USAGM da na Muryar Amurka," in ji shi.

Wakilan Fadar White House da na hukumar da kuma lauyoyin ma'aikatan da suka shigar da ƙara ba su yi saurin amsa bukatar jin ta bakinsu kan matakin ba.

Trump, wanda ya yi arangama da Muryar Amurka a wa'adinsa na farko, kana ya zabi Lake, wadda tsohuwar ‘yar jarida ce a matsayin daraktar hukumar USAGM a wa’adin mulkinsa na biyu.

Lake, wadda ta kasance babbar mai goyon bayan Shugaban Ƙasar, ta sha zargin manyan kafafen yada labarai da nuna ƙiyayya ga Trump.

Muryar Amurka wadda aka kafa ta a shekarar 1942 domin yakar farfagandar ‘yan Nazi, cikin mako ɗaya a shekarar 2024 mutane miliyan 360 ne suka saurari VOA, kamar yanda rahoton USAGM ga Majalisar kasar ya bayyana.

Lamberth, wanda Shugaba Ronald Reagan ya naɗa, ya saurari ƙararraki da dama wadanda ke kalubalantar sahihancin umarnin zartarwar Trump na watan Maris.

Ciki har da ƙarar da Michael Abramowitz, daraktan VOA ya shigar.