AFIRKA
2 minti karatu
A shirye Sojojin Sudan suke domin tattaunawa don dawo da zaman lafiya: Burhan
Kalaman na Burhan na zuwa ne gabanin fara taron ƙasashen Amurka da Saudiyya da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wanda za a yi a birnin New York domin lalubo mafita kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Sudan.
A shirye Sojojin Sudan suke domin tattaunawa don dawo da zaman lafiya: Burhan
Burhan ya jaddada cewa sojojin na Sudan za su ci gaba da yaƙar abokan gabarsu. / Reuters
14 awanni baya

Shugaban Majalisar Mulkin Sudan, Abdel Fattah al Burhan, ya bayyana cewa sojojin asar sun shirya tattaunawa don “kawo ƙarshen yaƙi da dawo da haɗin kai da martabar Sudan.”

Yayin da yake magana a Atbara da ke arewacin Sudan a ranar Asabar, yayin da yake yi wa iyalan wani jami’in soja, Muzammil Abdullah, ta’aziyya – wanda aka kashe kwanan nan a faɗa a Al Fasher, Burhan ya bayyana cewa babu wata tattaunawa da ake yi a halin yanzu da ƙasashe huɗu (Amurka, Saudiyya, Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa) ko wata ƙungiya daban.

Burhan ya jaddada cewa rundunar sojojin ƙasar “za ta ci gaba da yaƙar abokan gaba duk inda aka same su” kuma ya musanta zargin cewa suna kai hari kan ƙabilu ko yankuna.

Yakin da aka jima ana yi

Ya ce waɗanda suke neman zaman lafiya da gaske suna maraba da su, amma “tilasta zaman lafiya ko kafa gwamnati kan mutane ba tare da yardarsu ba abin ƙi ne.”

Waɗannan kalaman nasa sun zo ne kafin tarukan da ƙasashe huɗu suka shirya yi a birnin New York don ƙoƙarin samar da mafita mai dorewa ga yaƙin Sudan.

Sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun fara yaƙi tun watan Afrilun 2023, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 20,000 da kuma raba mutum miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin cikin gida.

A watan Yuli, Kungiyar Sudanese Founding Alliance, wata ƙungiya da RSF ke jagoranta, ta sanar da kafa wata gwamnati mai zaman kanta ƙarƙashin jagorancin shugaban RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda sojojin kasar suka yi Allah wadai da shi tare da ƙin amincewa da wannan mataki.