AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin da suka yi juyin mulki a Madagascar sun ce a shirye suke su tattauna da Tarayyar Afirka
"Ba mu yi mamakin matakin da aka ɗauka ba. (Amma) daga yanzu, za mu yi tattaunawar sulhu ta bayan-fage. Za mu ga yadda za ta kaya," in ji Kanar Michael Randrianirina.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Madagascar sun ce a shirye suke su tattauna da Tarayyar Afirka
Randrianirina ya ce zai sha rantsuwar kama aiki ranar Jumma'a a gaban kotun kundin tsarin mulki ta ƙasar / Reuters
15 awanni baya

Jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a Madagascar, Kanar Michael Randrianirina, ya ce a shirye yake ya tattauna da ƙungiyar Tarayyar Afirka, wadda ta dakatar da ƙasar daga cikinta saboda kifar da gwamnatin Andry Rajoelina.

"Ba mu yi mamakin matakin da aka ɗauka ba. (Amma) daga yanzu, za mu yi tattaunawar sulhu ta bayan-fage. Za mu ga yadda za ta kaya," in ji Kanar Michael Randrianirina a wani taron manema labarai da ya jagoranta ranar Alhamis.

Randrianirina ya ce zai sha rantsuwar kama aiki ranar Jumma’a a gaban Babbar Kotun Tsarin Mulki ta ƙasar a Antananarivo, babban birnin ƙasar.

Sai dai a ranar Alhamis, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin farar-hula a ƙasar, inda ya yi kira a dawo da tsarin mulki da doka.

"Ina yin tir da kawar da gwamnati da ƙarfin soji a Madagascar kuma ina kira a dawo da tsarin mulki da doka," a cewar Guterres a wata sanarwa da ya wallafa.

"Ina bayar da shawara ga dukkan masu rua da tsaki na Malagascar, ciki har da matasa su yi aiki tare domin magance matsalolin da suka haddasa yamutsi a ƙasar," in ji shi.

Ya ƙara da cewa a shriye MDD take ta yi aiki tare da ‘yan ƙasar da kuma neman goyon bayan ƙasashen duniya domin maido da tsarin mulki da oda.

Rajoelina, wanda ‘yan majalisar dokokin ƙasar suka tsige bayan ya tsere daga ƙasar, inda ya nuna fargaba game da yiwuwar halaka shi sakamakon zanga-zangar da matasa suka kwashe makonni suna yi wadda sojoji suka goyi bayanta, ya soki matakin Randrianirina na ɗarewa karagar mulki ƙasar.