Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike wa ‘yan kasar sakon ranar 1 ga Oktoba, a wani bangare na bukukuwan cika shekaru 65 da samun ‘yancin kasar daga Turawan Mulkin Mallaka na Ingila.
A sakon nasa, shugaban na Nijeriya ya fara bayyana muhimmancin da wannan rana ke da shi ga Nijeriya da ma ‘yan kasar.
Ga dai muhimman sakonnin da jawabin shugaban ke dauke da su:
Yaba wa ‘yan gwagwarmaya
Shugaba Tinubu ya ja hankalin ‘yan Nijeriya kan irin gudunmawa da sadaukar da kan da iyayen kasa na wancan lokacin suka yi don ganin Nijeriya ta samu ‘yancin kai.
Ya kuma bayyana yadda jagororin wannan lokacin ke da burin ganin Nijeriya ta zama kasa kuma jagora a Afirka, wadda za ta kasance fitila da abin koyi ga sauran kasashen duniya.
“A yayin da muke duba ga tafiyar kasarmu tun daga 1 ga Oktoban 1960, lokacin da iyayenmu suka karbi ragamar mulkin kasa daga ‘yan mulkin mallaka, ya kama mu tuna da sadakarwa, aiki tukurun da suka yi.
“Sannan mu sake tuna wa da burinsu samun ingantacciyar Nijeriya mai albarka da hadin kai da ta za ta jagoranci Afirka wajen zama fitila ga sauran duniya,” in ji Tinubu, a wata sanarwar da Mai Ba shi Shawara Kan Kafafen Yada Labarai Bayo Onanuga ya fitar ta shafinsa na X a ranar Larabar nan.
Shugaban na Nijeriya ya ci gaba da cewa jaruman kasar irin su Dr Nnamdi Azikiwe, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Chief Obafemi Awolowo, Sir Ahmadu Bello, Margaret Ekpo, Anthony Enahoro, Ladoke Akintola, Michael Okpara, Aminu Kano, Funmilayo Ransome-Kuti, da sauran ‘yan kishin kasa na da akidar cewa Nijeriya ce ta cancanci jagorantar dukkan bakaken fata a duniya.
Kalubale da nasarori cikin shekaru 65
Tinubu ya bayyana cewa tsawon shekaru da dama, burin da ake da shi bayan samun ‘yancin kai ya gamu da kalubale da dama a fannonin zamantakewa, tattalin arziki da siyasa, amma kasar ta tsira.
Ya kuma ce a yayin da ba lallai ne a ce Nijeriya ta samu cikar dukkan burinta ba, amma kasar ba yi nesa da su ba, yana bayyana cewar tun bayan samun ‘yancin kai shekaru 65 da suka gabata, Nijeriya ta samu cigaba sosai a fannin tattalin arziki, zaman tare da cigaban kayan more rayuwa.
Ya ce “A yau Nijeriya na bayar da ingantaccen ilimi da kula da lafiya sama da a 1960. A lokacin da aka samu ‘yancin kai, Nijeriya na da makarantun sakandire 120 ne kawai da daliban da ba su wuce 130,000 ba. Amma alkaluma sun nuna ya zuwa karshen 2024, akwai makarantun sakandire sama da 23,000 a kasarmu.”
Shugaban ya ci gaba da bayyana nasarar da kasar ta samu a bangare ilimi, inda ya ce a yanzu haka Nijeriya na da jami’o’i 274, kwalejojin fasaha 183 da na Ilimi 236 a Nijeriya, sabanin a 1960 da ake da Jami’ar Ibadan da Kwaljin yaba kawai.
Ya kara da cewa a kowane bangare an samu ci gaba. A bangaren lafiya, kayan more rayuwa, sha’anin kudade, samar da kayayyaki, sadarwa da cigaban yanar gizo, da sufurin jiragen sama da tsaro da ma sauran su.
Habaka tattalin arziki
Da yake tabo bangaren tattalin arziki da kayan bore rayuwa, shugaba Tinubu ya ce sun kudiri aniyar ci gaba da habaka wa da bunkasa Niejeriya domin samun walwala da jindadin ‘yan kasar.
“Bayan hawan mu mulki, mun gaji tattaln arzikin da ya kusa durkushe wa saboda shekaru da aka dauka ana ta’annatin kudade wanda ya janyo nakaru ga habakar tattalin arziki,” in ji shugaba Tinubu yana mai cewa a lokacin zabi biyu ne ya rage musu, ko su ci gaba da yin yadda ake yi, ko su dauki matakan gyara.
Ya ce gwamnatinsa ta dauki matsayin daukar matakin a sha wahala yau don a ji dadi gobe. A cikin kasa da shekaru uku, an fara girbar ‘ya’yan itatuwan alherin da aka shuka a baya.
Shugaban na Nijeriya ya kara da cewa daga cikin matakan da suka dauka har da cire tallafin man fetur da canjin kudaden kasashen waje mai yawa wadanda ke janyo tabarbarewar tattalin arziki.
Ya ce gwamnatinsu na kokacin ganin kowanne dan kasa ya amfana da arzikin Nijeriya, inda a yanzu akwa karkatar da kudaden da ake samu wajen inganta harkokin ilimi, kula da lafiya, tsaron kasa, ayyukan noma da kayan more rayuwa irin su hanyoyi, makamashi, layukan sadarwa da shirin zuba jari kan ‘yan kasa.
Tinubu ya bayar da tabbacin cewar dukkan wadannan matakai da suke dauka za su inganta rayuwar ‘ya Nijeriya, kuma sakamakon matakan da aka dauka, a yanzu gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi na samu albarkatu da yawa.
Shugaban ya kara da cewa a shekaru biyu da rabin da suka gabata, gwamnatin Nijeriya ta samu nasarori 12 a fannin tatalin arziki sakamakon kyakkyawan tsarin tasarrufin kudade da suke da shi.
Ya ce an samu karin kudaden shiga a bangaren da ba na man fetur ba, an samar da kyakkyawan tsarin tasarrufin kudade, asusun ajiya na kasashen waje na Nijeriya ya karu zuwa dala biliyan 42.03, mafi yawa tun shekarar 2019.
Haka zalika, Tinubu ya kuma ce Nijeriya ta zama mai fitar da kayayyaki tsantsa inda a yanzu kasar ta fi sayar da kayayyaki ga kasashen waje sama da wadanda take saya.
A sakon nasa, Tinubu ya kuma ce an dawo da fito da danyen mai ganga miliyan 1.68 kowace rana. Haka zalika an daidaita darajar kudin Naira a kasuwar canjin kudaden waje.. An kuma inganta hakar ma’adanin coal, tare da tallafa wa iyalai karkashin shirin zuba jari kan ‘yan kasa, da ma fadada wa da inganta harkokin sufuri a Nijeriya.
Ya ce “Ina farin shaida muku cewa a ƙarshe dai mun gano bakin zaren. Wahala ta zo ƙarshe, kamar yadda na ce.
A yanzu muna samun sauƙi daga matsalolinmu na baya. Ina jinjina muku saboda juriyarku da goyon baya da fahimtarku.
Zan ci gaba da yi muku aiki don saka muku kan amincewar da kuka yi mini na danƙa mini jagorancin jan ragamar ƙasar nan.
A ƙarƙashin jagorancinmu, tattalin arzikinmu yana farfaɗowa da sauri, kuma sauye-sauyen da muka fara a fiye da shekara biyu suna samar da kyawawan sakamako.
Ma’aunin Tattlin Arzikin Kasa na GDP ya haɓaka da kashi 4. 23% a cikin rubu'i na biyu na shekarar 2025 — wadda ita ce haɓaka mafi sauri da Nijeriya ta gani a cikin shekara huɗu da suka wuce — har ma ta wuce haɓakar da Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF ya yi hasashe na kashi 3.2%..
Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 20.12% a watan Agustan 2025, mafi ƙarancin hauhawa da aka samu a cikin shekara uku.
Gwamnatin nan tana aiki ka’in-da-na’in don bunƙasa samar da amfanin gona da tabbatar da samar da wadataccen abinci da rage farashin kayayyakin abinci.”
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana yadda duniya ke shaida kokarinsu inda hukumomin bayar da lamuni suka daga darajar Nijeriya da yadda suke kallon kasar. Duk hakan na zuwa ne sakamakon kokarin gwamnatinsa na habaka tattalin arziki.
Sakon Tinubu na ranar samun ‘yancin kan Nijeriya ya kuma ce kamar yadda babban bankin Nijeriya ya rage kudin ruwa a karon farko a cikin shekaru biyar, kasuwar hannayen jarin Nijeriya ma na burunkara sosai inda ta daga daga maki 55,000 a 2003 zuwa 142,000 a watan Satumban 2025.
Inganta Tsaro:
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsu na aiki don inganta tsaron kasa. Jam’ian soji da sauran hukumomin tsaro na aiki ba gajiyawa tare da yin sadaukarwa don kare kasarmu.
Ya ce jami’an tsaron Nijeriya na samun nararori wajen yaki da ta’addanci, ‘yan bindiga da sauran muggan laifuka.
“Muna ganin irin nasarar da suke yi a yadda suka murkushe Boko Haram a arewa maso-gabas, IPOB/ESN a kudu maso-gabas da garkuwa da mutane da ayyukan ‘yan bindiga,” Tinubu ya bayyana haka inda ya ce dole ne a yaba wa jami’an tsaron Nijeriya tare da jinjina musu.
Cigaban matasa
Shugaba Tinubu ya ce yana da sako ga matasan Nijeriya inda ya bayyana su a matsayin kadarorin kasar mai albarka.
“Dole ne ku ci gaba da yin babban mafarki, ƙirƙira, da cin nasara a wasu yankuna a fannonin kimiyya, fasaha, wasanni da fasahar kere-kere.
Gwamnatinmu, ta hanyar manufofi da kudade, za ta ci gaba da ba ku fuka-fuki don tashi sama,” in ji Tinubu a yayin da yake karfafa gwiwar matasan Nijeriya.
Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta kirkiro NELFUND don tallafawa ɗalibai da lamuni don neman ilimi.
Kimanin dalibai 510,000 a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ne suka ci gajiyar wannan shirin, wanda ya kunshi manyan makarantu 228.
Ya ce ya zuwa ranar 10 ga watan Satumba, jimillar lamunin da aka bayar ya kai na Naira biliyan 99.5, yayin da alawus kuma ya kai Naira biliyan 44.7.
Haka zalika ya bayyana shirinsu na Credicorp, wani shiri ne na gwamnatin Nijeriya da ya baiwa ‘yan kasar 153,000 rancen kudi Naira biliyan 30.
Sai an sha wuya a kan sha dadi
Da yake rarrashin ‘yan Nijeriya game da wahalar da aka shiga sakamakon wasu manufofin gyara da gwamnatinsa ta dauka, shugaba Tinubu ya ce “A kodayaushe na yarda cewa wadannan gyare-gyaren sun zo da wasu radadi.
Tabarbarewar hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa sun kasance babban abin damuwa ga gwamnatinmu.
Amma, maimakon mu bar bar kasarmu ta fada cikin rudanin tattalin arziki ko kuma fatara ba abu ne da zai dace ba, hakan ya samu daukar matakan gyara.”
A karshe Shugaba Tinubu ya yi kira ga ‘yan kasar da su jajirce wajen yin aiki tukuru, sannan su ba wa gwamnatinsa goyon bayan don gudanar da ayyukan cigaba.