AFIRKA
4 MINTI KARATU
Jadawalin bikin mika mulki daga Shugaba Buhari zuwa Bola Tinubu
Gwamnatin Nijeriya ta fitar da tsarin bikin mika mulki na mako daya tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da shugaba mai jiran gado Bola Tinubu.
Jadawalin bikin mika mulki daga Shugaba Buhari zuwa Bola Tinubu
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari (Hagu) zai mika mulki ga Bola Tinubu (Dama)  ranar 29 ga watan Mayunn 2023. Hoto: Reuters
19 Mayu 2023

Gwamnatin Nijeriya ta fitar da jadawalin mako daya na bikin mika wa zababben shugaban kasar Bola Tinubu mulki ranar 29 ga watan Mayu don zama shugaban kasar na 16.

Sakataren Gwamnatin kasar kuma shugaban kwamitin mika mulki, Boss Mustapha, ya bayyana ranar Alhamis cewa za a yi shagali na mako daya zuwa 29 ga watan Mayu ranar da Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ga shugaba mai jiran gado Bola Tinubu.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar Boss Mustapha ya ce ranar Talata, 23 ga watan Mayu 23, za a yi liyafa ta girmamawa ta soji ga shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari.

Ranar 24 ga watan Mayu 24 (Laraba), za a yi taron bankwana na Majalisar Ministoci a Fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kazalika ranar 25 ga watan Mayu (Alhamis), za a karrama Tinubu da babban lambar yabo ta GCFR da ake bai wa shugabannin kasa kadai. Har wa yau a ranar, Buhari zai karbi lambar yabo ta GCON da ake bai wa tsofaffin shugabannin kasar. A yayin bikin, Buhari zai mika takardun mika mulki ga Tinubu.

Ba na neman mukami a gwamnatin Tinubu - Elrufai

A ranar 26 ga watan Mayu (Juma'a), za a gabatar da lacca da sallar Juma'a a babban masallacin kasa da ke Abuja tsakanin karfe 10 na safe zuwa 1:30 na rana.

A ranar 27 ga watan Mayu (Asabar), Tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, zai ba da lacca kan "hanyoyin zurfafa dimokuradiyya don cudanya da ci gaba".

A ranar 28 ga watan Mayu (Lahadi), za a gudanar da taro na mabiya addinin Kirista a cibiyar kiristoci ta kasa da ke Abuja. A yammacin ranar, Shugaba Buhari zai karbi bakuncin baki da suka zo don a yi liyafar cin abincin dare a dakin taro na fadar gwamnati.

A ranar 29 ga Mayu (Litinin), Tinubu zai yi rantsuwar kama aiki a dandalin Eagle Square da ke Abuja da misalin karfe 10 na safe agogon kasar. Haka kuma za a gudanar da faretin kaddamarwa.

Sannan kuma za a gudanar da liyafar cin abincin rana bayan rantsar da shi a dakin taro na Banquet House da misalin karfe 1:30 na rana. Tinubu ne ya shirya liyafar, kuma ana sa ran shugabannin kasashen da aka gayyato da shugabannin gwamnati da manyan baki ne kawai za su halarci taron.

Kwamitin mika mulki ya ce an gayyaci shugabannin kasashe da na gwamnati da dama, kuma akasarinsu sun ba da tabbacin cewa za su halarci bikin mika mulkin Nijeriya ga Bola Tinubu.

Shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya ce ba zai iya bayyana adadin ko sunayen shugabannin da aka gayyata ba saboda “sha'ani na tsaro”.

Tinubu, wanda ya yi takara a jam’iyyar APC mai rike da mulki, ya samu kuri’u miliyan 8.8 kuma an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Nijeriya da aka gudanar a watan Fabrairun 2023.

Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya zo na biyu da kuri'u miliyan 7, yayin da Peter Obi na jam'iyyar Labour ya zo na uku da kuri'u miliyan 6.1.

Atiku da Obi sun yi wasti da sakamakon zaben, kuma sun shigar da kara a gaban kotun zabe, suna kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci
Rundunar RSF ta amsa aikata 'take haƙƙi' a Al Fasher na Sudan
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 11 'yan yawon bude ido a hatsarin jirgin da aka yi a kasar