Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya ɗauki matakin gaggawa na ba da ikon samar da rundunar kiyaye tsaro ta ƙasa da ƙasa a Gaza, tana mai cewa jinkiri zai iya lalata shirin zaman lafiya mai rauni da Amurka ke mara wa baya.
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya shaida wa kafar watsa labarai ta The National da ke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ranar Litinin cewa mahukunta a Alƙahira suna goyon bayan samar da wata runduna ta kiyaye zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa da kuma wata “Majalisar Zaman lafiya” domin jagorantar kai kayan agaji da kuma sa ido kan sake gini a Zirin Gaza da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Shirin da aka tsara, wanda wani ɓangare ne na shirin da Amurka ta jagoranta da Shugaba Donald Trump ya gabatar, yana da niyyar samar da wani tsari na mataki-mataki bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta ranar 10 ga watan Oktoba ciki har da miƙa makamai na ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas da kuma gabatar da runduna ta ƙasa da ƙasa.
Abdelatty ya jaddada cewa dole Gaza ta kasance ƙarƙashin ikon gwamnatin Falasɗinawa, amma ƙudurin MDD na da mahimmanci wajen samar da “halacci” ga rundunar kiyaye zaman lafiya da kuma bayyana aikinta.
"Ya kamata manufar ta kasance kiyaye zaman lafiya ba tilasta zaman lafiya ba," a cewarsa, yana mai ƙarawa da cewa rundunar zaman lafiyar ta ƙasa da ƙasa da "Majalisar Zaman lafiya " — wadda ake tsammanin za ta ƙunshi mutanen kamar su tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair — za su taimaka wajen aikin ‘yan sanda da aikin gwamnati da kuma gabatar da agaji na ƙasa da ƙasa.
Kalaman na zuwa ne yayin da Amurka ke nuna damuwa game da yiwuwar rashin zaman lafiya nan gaba inda ziyarar mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ta baya bayan nan zuwa Isra’ila ta yi kiciɓis da fargabar cewa Netanyahu zai iya kawo ƙarshen tsagaita wuta ya kuma ci gaba da yaƙi a Gaza.