AFIRKA
2 minti karatu
Sojin Sudan sun yi wa ‘yan ta’adda mummunar ɓarna bayan hari a Al Fasher
Rundunar sojin Sudan tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda sun tare maharan inda suka kashe da yawa daga cikinsu.
Sojin Sudan sun yi wa ‘yan ta’adda mummunar ɓarna  bayan hari a Al Fasher
Wuraren da dakarun RSF ke riƙe da su sun ragu cikin sauri kwanan nan a faɗin Sudan yayin da soji ta faɗaɗa nasarorinta na soji. / AA
20 Oktoba 2025

Rundunar sojin Sudan ta ce dakarunta sun daƙile wani gagarumin hari kan birnin Al Fasher da “mayaƙan ‘yan ta’adda” suka kai, bayan musayar wuta mai muni da ta kashe gomman mahara kuma ta tilasta wa sauran ja da baya, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Sudana (SUNA) ya ruwaito.

Wata sanarwa daga rundunar sojojin ƙasar ta ce an fara harin ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare ranar Lahadi, lokacin da wasu ‘yan ta’adda suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin makarantar horas da soji domin kai wa ga hedikwatar rundunar wadda aka fi sani da “Sansanin Jajircewa.”

Rundunar sojin Sudan, wadda take aiki tare da ‘yan sanda, ta tare maharan, inda ta yi musu ɓarna mai yawa da kuma lalata wasu daga cikin motocinsu.

A wata sanarwar, rundunar sojin ta yaba da “jarumta da jajircewar” masu kare birnin, inda ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan sojojin da suka mutu tare da fatan samun sauƙi cikin sauri ga waɗanda suka jikkata.

Rundunar sojin ta ce sauran ‘yan ta’addan sun tsere kudancin birnin bayan “rasa rayuka da kayayyaki masu yawa.” Rundunar sojin dai ba ta bayyana sunayen waɗanda suka kai harin ba.

Sai dai, rundunar sojin Sudan da dakarun RSF sun ƙaddamar da yaƙi a tsakaninsu tun watan Afrilun shekarar 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20,000 da kuma raba mutum miliyan 14 da gidajensu, in ji Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin cikin ƙasar.

Hare-haren ramuwar gayya

Sanarwar ta ƙara da cewa maharan, sun zafafa luguden wuta da manyan bindigogi  kan cibiyoyin soji da fararen-hula a arewa da gabashin Al Fasher, kusa da makarantar sakandare ta Al-Zareeba da Darfur.

Sai dai kuma, an tunkari harin da abin da rundunar sojin ta kira “martani ƙwaƙƙwara,” lamarin da ya janyo mutuwar manyan mayaƙan ‘yan ta’adda da kwamandoji.

“Har yanzu Al Fasher wani wuri ne da ba za a iya kutsawa ba,” kamar yadda rundunar sojin ta bayyana, tana mai alƙawarin cewa “mazaje masu ƙarfin zuciya da kuma yaƙi da zuƙatansu” za su ci gaba da kare birnin.