AFIRKA
2 minti karatu
Nnamdi Kanu: ‘Yan sanda a Abuja sun tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki jagoran IPOB na Nijeriya
‘Yan sandan Nijeriya sun harba hayaki mai sa hawaye a ranar Litinin tare da mamaye manyan hanyoyin babban birnin Abuja don dakatar da zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare shugaban ‘yan ta’addar aware na Biafra IPOB Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu: ‘Yan sanda a Abuja sun tarwatsa masu zanga-zangar neman a saki jagoran IPOB na Nijeriya
Ana tuhumar jagoran 'yan ta'addar IPOB Nnamdi Kanu da laifukan ta'addanci. / REUTERS
20 Oktoba 2025

‘Yan sandan Nijeriya sun harba hayaki mai sa hawaye a ranar Litinin tare da mamaye manyan hanyoyin babban birnin Abuja don dakatar da zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare shugaban ‘yan ta’addar aware na Biafra IPOB Nnamdi Kanu.

Kanu wanda ke da shaidar zama dan kasar Birtaniya, yana jagorantar haramtacciyar kungiyar IPOB da ke fafutukar ballewar yankin kudu maso-gabashin Nijeriya, inda akasarin su ‘yan kabilar Igbo ne.

A tsakiyar birnin Abuja, 'yan sanda dauke da makamai sun yi sintiri tare da motocin watsa ruwa da manyan motoci masu sulke, suka dinga harba hayaƙi mai sa hawaye a wajen da masu zanga-zangar suka yi kokarin taruwa.

A wasu sassan birnin kuma, sojoji dauke da makamai sun mara wa ‘yan sanda baya ta hanyar nuna ƙwanji.

Masu zanga-zangar da suka hada da masu fafutukar kare hakkin ɗan’adam da kuma masu rajin kare dimokuradiyya, wani bangare ne na gangamin da ke neman a saki Nnamdi Kanu.

Sannan suna kokarin tirsasa Gwamnatin Tarayya ta yi aiki da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na 2022 da ta wanke Kanu tare da ba da umarnin a sake shi.

Magoya bayan Kanu sun ce tsare shi tun shekarar 2021 na da nasaba da siyasa kuma suna son a sake shi tare da wanke tuhume-tuhume bakwai na ta’addanci da ake yi masa.

Kanu dai ya ƙi amsa laifin da ake tuhumar sa da shi, wanda ke dauke da hukuncin ɗaurin rai da rai.