AFIRKA
1 minti karatu
Dakarun tsaron Nijar sun kashe ‘yan ta’adda a Jihar Dosso
Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce lamarin ya auku ne a lokacin da wasu ‘yan ta’adda ɗauke da makamai bisa babura suka yi wa dakarun tsaron ƙasar kwanton-ɓauna da bai yi nasara ba.
Dakarun tsaron Nijar sun kashe ‘yan ta’adda a Jihar Dosso
Dakarun tsaron Nijar suna ƙoƙarin yaƙar 'yan ta'dda da ke kai hare-hare kan sojoji da fararen hula a ƙasar / Sojin Nijeriya
20 Oktoba 2025

Dakarun tsaron Jamhuriyar Nijar sun kashe ‘yan ta’adda biyu a kudu maso yammacin Bolbol da ke Jihar Dosso, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka rawaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne a lokacin da wasu ‘yan ta’adda ɗauke da makamai bisa babura suka yi wa dakarun tsaron ƙasar kwanton-ɓauna.

Sai dai dakarun sun nuna ƙwarewa inda suka yi musayar wuta da ‘yan ta’addan lamarin da ya kai ga kashe biyu daga cikin jgororinsu.

Hakan ya sa sauran ‘yan ta’addan sun tsere zuwa ƙasa mai maƙwabtaka kuma suka bar kayayyakinsu.

Binciken da sojoji suka gudanar baayan arangamar ya kai ga samo kayayyaki da yawa ciki har da babur ɗaya da bindigogi ƙirar AK47 da rokoki biyu ƙirar RPG-7  da ƙwanson harsasai 18 na bindiga ƙirar Kalashnikov da wata wayar salula ƙirar Motorola da sauran kayayyaki.

Kafar Actu Nijar ta ambato majiyoyin tsaro suna cewa babu wani jam’in tsaro da ya jikkata ko ya rasa ransa sakamakon ba-ta-kashin.