Hawan jini: Kawar da mummunan giɓin kula da lafiya a Afirka
AFIRKA
5 minti karatu
Hawan jini: Kawar da mummunan giɓin kula da lafiya a AfirkaCutar hawan jini na ƙara yawaita a Afirka da ma wajen nahiyar, cutar da cikin sirri ke kashe rayuka miliyan 10 kowace shekara a duniya, a yayin da tsarin kula da lafiya ke gwagwarmayar samar da kulawa ga wadanda ke cikin hatsari.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce mutum daya cikin mutane 5 a duniya ne kadai ke samun damar kula da hawan jininsu. Hoto: WHO/Tafadzwa Ufumeli / Others
15 awanni baya

Ɗan Nijeriya Michael Adeyemi yana tuƙa tasi dinsa ta wani titin da aka saba ganin cunkoso a Legas lokacin da jiri ya kama shi.

Direban mai shekaru 58 ya ja baya, ya damƙe sitiyarin motar a yayin da kansa ke juyawa.

Ya yi biris da ciwon kan tsawon watanni. Haka ma gajiyar. Tsawon sa'o'i yana tafiya a cikin birni wanda ba ya tsayawa, ya ci a ce ya yi tunani da kansa.

Amma wannan abu ya zama na daban.

"Ina tsammanin gajiya da damuwa ne kawai, sakamon rayuwa a cikin birni mai cike da cunkoso," Adeyemi ya shaida wa TRT Afrika.

"Ba mu da lokacin rashin lafiya. Kuna aiki, kuna samun na abinci, kuna barci. Duba hawan jinin ku abin jin daɗi ne da kuka ware wa ranar Asabar da ba ta zo ba."

Kamuwa da jiri nan da nan yayin tuki ya nuna alamun kamu wa cutar hawan jini ga Adeyemi, inda ya shiga jerin mutane biliyan 1.4 da ke fama da cutar, a cewar rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da aka fitar a bara.

Dalilai na gama-gari

Alkaluman na WHO sun bayyana wani yanayi na gaggawa na kiwon lafiya da ke boye a fili: daya daga cikin mutane biyar a duk duniya kadai ke kula da hawan jininsu.

Duk da yake ana iya riga-kafin cutar da ake kira "mai kisa a sirrance" ta hanyar likitanci kuma ana iya magance ta, tana kasance wa mai hatsarin gaske idan ba a yi maganinta a kan kari ba.

Likitoci sun yi gargadin cewa sakamakon rashin kula da cutar hawan jini yana da tsanani. Hawan jini yana haifar da bugun zuciya, bugun jini, gazawar koda da hauka.

Bayanan da aka fitar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80, sun bayyana gibi da rashin daidaito a fannin kiwon lafiya.

Rahoton ya nuna cewa kashi 93 cikin 100 na kasashen da ke da yawan kudin shiga suna da dukkan magungunan hawan jini da WHO ta ba da shawarar amfani da su, sabanin kashi 28% na kasashe masu karamin karfi.

Wannan rata tsakanin kasashe masu arziki da matalauta na nufin miliyoyi mutane na fuskantar mutuwar da za a iya kawar wa da kuma nakasa sakamakon cututtuka masu alaƙa da hawan jini.

Rayuwa marar dadi

Grace Mbeki, wata malama ‘yar shekara 42 da ke zaune a wani gari da ke wajen birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, ta yi taka-tsan-tsan wajen kula da cutar hawan jini yayin da take kula da mahaifiyarta, wadda ta yi fama da lalurar shanyewar jiki sakamakon hawan jinin.

“Asibitin na da nisa daga gidana, kuma a wasu lokutan sai na dawo ba tare da maganin da aka rubuta min ba saboda ya kare,” Mbeki ta shaida wa TRT Afrika.

"An bar ku kuna kallon wanda kuke so ya zama inuwa. Wannan cutar ba kawai tana karya zuciya ba ne, tana karya iyalai da kudadensu."

Zafin da ke cikin kalamanta na bayyana gwagwarmayar yau da kullum na kula da yanayi na yau da kullum a tsarin kiwon lafiya da ke fama da buƙatu kuma magunguna suna ɓacewa daga ɗakunan ajiya ba tare da gargadi ba.

Nauyin tattalin arziki

Tsakanin 2011 da 2025, an yi hasashen cututtukan da suka shafi zuciya za su janyo wa ƙasashe masu matsakaicin samun kudi da matalauta kashe kusan dalar Amurka tiriliyan 3.7.

Wannan yana bayyana dimbin kuɗaɗen da aka wawure daga asusun ajiyar kuɗi, da karkatar da albarkatu daga ilimi, ababen more rayuwa da cigaban tattalin arziki.

"Kowace sa'a, sama da rayuka 1,000 ne ke mutuwa sakamakon shanyewar jiki da bugun zuciya wadanda hawan jini ke janyo wa, kuma galibin wadannan mace-mace ana iya yin riga-kafinsu," in ji babban daraktan WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.

"Ƙasashe suna buƙatar samun kayan aikin da za su canza wannan lamari."

Rahoton ya yi nuni da yadda manufofin inganta kiwon lafiya marasa karfi ke barin al'umma ba su san illar shan taba da kuma cin abinci mai gishiri da yawa ba, wanda dukkansu ke kara tsananta hawan jini.

Wani abu kuma shi ne ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan kulawa a matakin farko wanda hakan ke kawo cikas ga gano cutar da wuri da zuwa ga likita yadda ya kamata.

Ga marasa lafiya kamar Adeyemi da Mbeki, waɗannan gazawar na bayyana rashin tabbas da hatsarin yau da kullum.

"Hawan jini da ba a kula da shi ba yana kashe rayuka sama da miliyan 10 a duk shekara duk da cewa ana iya yin riga-kafi da kuma magance su," in ji Dr Kelly Henning na Bloomberg Philanthropies.

"Samar da manufofi masu karfi da ke kara wayar da kan jama'a da kuma fadada hanyoyin samun magani suna da mahimmanci."

Mataki daya a lokaci guda

WHO ta yaba wa kasashen Asiya kamar su Bangladesh, Philippines da Koriya ta Kudu saboda samun gagarumin cigaba wajen dakile annobar cutar hawan jini ta hanyar shigar da kula da hawan jini a cikin tsarin kiwon lafiya na duniya da tsarin kula da lafiya a matsakin farko.

A Bangladesh, duba hawan jini a wasu yankuna ya karu daga kashi 15% zuwa 56% cikin ‘ƴan shekaru kaɗan, wanda hakan ke bayyana nasarorin da za a cim ma idan aka samar da kyawawan manufofi da aiwatar da su.

Dokta Tom Frieden, wani babban likita a Amurka ya ce "Akwai magunguna masu aminci, masu rahusa don kula da hawan jini, amma mutane da yawa ba za su iya samun su ba."

"Rufe wannan gibin zai ceci rayuka, da kuma ceton biliyoyin daloli a duk shekara."

A batun Adeyemi, wannan gibin na bayyana tazarar da ke tsakanin motar tasi ɗinsa da amintattun magunguna masu arha. Yanzu yana ɗaukar magungunansa ko'ina zai je.

"Ina daya daga cikin masu sa'a" ya bayyana hannunsa a kan zuciyarsa. "Na samu gargadi. Amma miliyoyin da ba su yi ba fa?

“Muna bukatar duniya ta ji bugun zuciyarmu kafin su daina harba wa."