Nijeriya na ta ɗaukar hatsarin gwajin yin jarrabawa ta hanyar amfani da kwamfuta
AFIRKA
5 minti karatu
Nijeriya na ta ɗaukar hatsarin gwajin yin jarrabawa ta hanyar amfani da kwamfutaRubuta jarraba wa da kwamfuta na rage satar amsar jarrabawar neman shiga jami’o’in Nijeriya, amma wani abu da ya sace gwiwar dubunnai ya kawo tambaya kan gaggawar aiki da tsarin wajen rubuta jarrabawar kammala sakandire nan da 2026.
Nan da shekarar 2026, za a gudanar da dukkan jarrabawar kammala Sakandire a cibiyoyin ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta. / TRT Afrika
11 awanni baya

Jajayen idanuwan Farfesa Ishaq Oloyede ne ke bayar da labarin kafin kalaman masa su fito daga bakinsa. Ya tsinci kansa a cikin takura.

Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta Najeriya (JAMB) Oloyede ya tsaya a gaban kyamarorin manema labarai a watan Mayun 2025 domin neman afuwar wani babban kuskuren fasaha da ya janyo rashin nasara ga dubban ‘yan takarar shiga jami’aa kasar.

“A matsayina na magatakardar JAMB, ina dora alhakin duk abinda ya faru a kaina ciki har da sakaci na rashin kyawun na’orori,” in ji shi a wani faifan bidiyo da ya yadu a yanar gizo. “Ina ba da hakuri game da wannan abu marar dadi musamman irin halin kuncin da ya jefa ‘yan Najeriya kai tsaye ko akasun haka.”

Matsalar ta haifar da gazawar da ba a saba gani ba a sakamakon jarrabawar neman shiga manyan makarantu (UTME), wacce JAMB ke gudanarwa don tantance gurbin shiga jami'o'i a fadin Najeriya.

A lokacin masu rubuta jarrabawa suka koka, da farko wasu jami’ai da suka hada da Ministan Ilimi Tunji Alausa, sun danganta rashin nasarar da aka samu ba ga wasu kura-kurai na fasaha ba, illa dai dakile satar jarrabawa ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta.

“JAMB na gudanar da jarrabawarta ne ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa, sun samar da tsauraran matakan tsaro, don haka an kawar da zamba ko satar amsa gaba daya. Abin takaici, ba za mu iya fadin hakan ga WAEC ko NECO ba,” in ji Ministan.

WAEC da NECO na gudanar da Jarrabawar shaidar kammala Sakandare (SSCE) a Najeriya. Kyakkyawan sakamako a cikin daya daga jarrabawowin, ko duka biyun, na daga sharuddan farko na samun gurbin shiga jami’a ko wata babbar makarantar gaba da sakandire.

"Dole ne mu yi amfani da fasaha don yakar wannan zamba," in ji Alausa. "Akwai 'cibiyoyin mu’ujiza’ (miracle centres) da yawa, kuma hakan ba abin yarda ba ne kawai, mutane suna satar amsa a lokacin jarrabawar WAEC da NECO, sannan su fuskanci JAMB, inda da wahala a iya yin satar amsa. Wannan ne bambancin da muke gani a yanzu haka. Abin takaici ne.”

Shirin kai kayan aiki

Watanni bayan takaddamar sakamakon UTME, ana ƙarfafa ra'ayin yin amfani da kwamfuta a jarrabawar kammala makarantun sakandire.

A baya-bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin sauya dukkan jarrabawar kammala sakandire musamman WAEC da NECO daga rubutu a takarda zuwa ta amfani da na’urar kwamfuta nan da shekarar 2026.

Minista Alausa ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar sa ido ga rubuta jarrawabar SSCE ta farko da na’urar kwamfuta a makarantar sakandire ta Sascon International School da ke Abuja.

Wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar Folasade Boriowo, ta ambato ministan na bayyana jarrabawar a matsayin wata gagarumar ‘yar manune ga yiwuwar tabbatar da hakan da ma yin shiri a nan gaba.

Ministan ya bayyana cewa nan da shekarar 2026, za a gudanar da dukkan jarrabawar kammala Sakandire a cibiyoyin ta hanyar amfani da na’urar kwamfuta.

Damuwa game da kayan aiki

Masana na ganin sauyin sheka daga rubuta jarrabawar da alkalami a takarda zuwa amfani da na’urar kwamfuta ga dalibai kusan miliyan biyu na iya fuskantar cikas a kasar da da ke da matsalar kayan aiki saboda rashin wutar lantarki da yanar gizo.

Tsadar saka kwamfutoci masu amfani da yanar gizo na iya zama kalubalen hana wasu makarantar samun kayan aiki, a cewar kungiyar masu cibiyoyin jarabawa da na\ura mai kwakwalwa ta Najeriya (CPAN).

Austin Chinedu Ohaekelem, shugaban kungiyar na kasa, ya yi imanin cewa makarantu kadan ne za su iya samar da ingantattun dakunan karatu masu na’urorin kwamfuta.

Har ila yau, tafiya zuwa wuraren da aka keɓe na rubuta jarraba da kwamfuta, musamman daga ƙauyuka masu nisa, na iya zama cikas. "Duk da cewa hakan ba zai yi wahala ba wajen gudanar da jarrabawar da ake yi rana guda, amma ana daukar makonni kafin a kammala jarrabawar kammala sakandare," Ohaekelem ya shaida wa TRT Afrika.

Wani batu da ya kamata a warware shi shi ne, samar da kwararrun ma’aikatan fasaha da za su tafiyar da sarkakiyar gudanar da irin wadannan jarrabawa da jadawalin darussa da ma daliban da za su rubuta jarrabawar.

Manufofi da za a iya cim mawa

Duk da matsalolin da ke tattare da sauya sheka zuwa tsarin da ke tattare da kalubale na fasaha da na kayan aiki, kungiyar ta CPAN ta nuna goyon ga ministan ilimi Alausa game da yiwuwar sauya shekar daga jarrabawa da alkalami da takarda zuwa amfani da kwamfuta.

"Kamar yadda na fada a baya, babu wani sabon abu game da jarrabawa ta kwamfuta, ba tare da la'akari da inda kake a Najeriya ba," in ji Ohaekelem. "Yawancin dalibai suna amfani da na'urorin tafi-da-gidanka da yanar gizo."

Duk da cewa hakan na iya zama ba gaskiya ba ga yaran da suka fito daga gidajen da ba su da karfin tattalin arziki, masu gudanar da cibiyoyi da gwamnati na duba yiwuwar aiki da tsarin rubuta jarrabawar shiga jami'a ta amfani da kwamfuta zuwa ga rubuta SSCE.

Masana sun ce yadda masu ruwa da tsaki za su koyi darasi daga matsalolin da hukumar ta JAMB ke fuskanta zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance ko za a iya bunkasa tsarin a yanzu.