AFIRKA
2 minti karatu
Mayaƙan RSF sun kai hari da jirage maras matuƙa a filin jiragen saman Khartoum gabanin sake buɗe shi
Harin na zuwa ne kwana ɗaya tak kafin a sake buɗe babban filin jiragen saman Sudan fiye da shekaru biyu bayan an rufe shi.
Mayaƙan RSF sun kai hari da jirage maras matuƙa a filin jiragen saman Khartoum gabanin sake buɗe shi
Harin dai an kai shi ne da zummar hana sake buɗe filin sauƙa da tashin jiragen da aka daɗe ana jinkirtawa / AP
19 awanni baya

Mayaƙan RSF sun ƙaddamar da hare-hare na jirage maras matuƙa kan muhimman wurare a babban birnin Sudan, inda suka mayar da hankali kan filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Khartoum da kuma wata tashar wutar lantarki, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Shaidun da kafar watsa labarai ta Rakoba News ta ambato ranar Talata sun ce an ji ƙarar fashewar ababe aƙalla takwas a ciki da kusa da filin jiragen, filin da hukumar sufurin jiragen sama ta ƙasar ke shirin buɗewa a ranar Laraba, a karon farko da zai yi aiki tun lokacin da aka fara yaƙin kimanin watanni 30 da suka gabata.

Da alama an ƙaddamar da harin ne domin hana sake buɗe filin jirgin saman da aka daɗe ana jinkirtawa, in ji kafar. 

An harbo jirage maras matuƙa

Rahotannin sun ce sojojin Sudan sun harbo wasu daga cikin jiragen maras matuƙa, amma wasu daga cikinsu sun kai ga inda aka tura su, inda suka lalata ababe da kuma sanya fargaba a zukatan mutanen da ke unguwannin da ke maƙwabta.

Rundunar sojin ƙasar da dakarun RSF ba su yi tsokacin kan lamarin ba har zuwa lokacin rubuta wannan labarin.

Rundunar Sojin Sudan ta bayyana a watan Maris cewa ta karɓe iko da filin jiragen sama na Khartoum da wasu gundumomi da ke kewaye da shi a karon farko tun da yaƙi ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu a watan Afrilun shekarar 2023.

Rikicin da ake yi ya kashe fiye da mutum 20,000 tare da raba mutum miliyan 14 million da gidajensu, in ji Majalisar Dinkin Duniya, ɗaya daga cikin bala’i mafi muni a duniya.