Rikicin kabilanci da aka kwashe kusan shekaru bakwai ana yi a yankunan Arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru ya yi matukar gurgunta sashen ilimi na kasar.
A wani rahoto da kamfanin dillacin labarai na Kamaru CNA ya fitar, an bayyana cewa dubban yaran da iyayensu ba su da hanya ko karfin tserewa zuwa wauraren da za su samu mafaka sun fada cikin wani yanayi sakamakon rashin zuwansu makarantu don samun ilimi.
‘’Galibin yaran suna yankunan da rikice-rikicen ta’addanci da na kabilancin suka fi kamari ne,’’ a cewar CNA
Wasu daga cikin yara matan sun zama iyaye, sai dai ba haka lamarin yake ba ga Achang Winifred, wata yarinya ‘yar shekara 16 da ta fito daga garin Kom-Boyo da ke yankin Arewa maso Yamma na kasar.
''Achang ta koma makaranta bayan mahaifinta ya yi nasarar tura ta Douala,'' in ji rahoton CNA
A shekara 16, ya kamata ta kammala karatunta na aji shida a matakin makarantar firamare amma saboda rikicin, ba ta karasa ba balle ta kai ga zuwa sakandare.
Sai dai duk da koma bayan da Achang ta samu a karatunta ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana farin cikinta na komawa makaranta a Douala, yayin da ta shiga aji daya na babbar makarantar sakandare ta “Atalanta Bilingual Comprehensive High School” da ke Bonaberi.
“Na kwashe shekara biyar ban je makaranta ba saboda tashe-tashen hankulan da ake fama da su. Hakan ya zame mana wani babban kalubale, domin wasu daga cikin 'yan mata kamar ni a yanzu sun zama iyaye, wasu ba sa iya ko jin Turanci mai kyau. Ba su san komai ba," a cewar Angang Winifred.
Achang ta bayyana cewa hare-haren da ake kai wa makarantu da malamai da dalibai ya jinkirtar tare da gurgunta burinsu.
“Ina da burin zuwa makaranta da fita zuwa wata kasa da kuma aiki da kula da iyayena. Amma ban kai ga cimma hakan kakamakon rikicin da ya gurgunta makarantu a kasarmu, dole na zauna a gida," a cewar Achang a yayin zantawarta da CNA a Douala babbar birnin Kamaru.
Wani dalibi dan gudun hijira dan shekara 17 da a yanzu ya shiga aji biyu na sakandare maimakon aji uku, ya ce ya tsere wa harbe-harben bindiga a kauyen Wei da ke yankin Boyo domin ya samu damar ci gaba da karatunsa a Douala.
“Saboda rikicin, shekara uku kenan ban je makaranta ba sai yanzu. A tsawon shekarun na yanke shawarar zuwa gareji don rage radadin rashin karatu, na yi fatan wata rana zan samu damar ci gaba da karatu ga shi kuwa yanzu na samu," in ji shi.
Dalibin ya bayyana cewa da yake kauye ana yawan harbe-harbe a duk lokacin da suka je makaranta, hakan ya tilasta musu barin makaranta, ‘’wasu lokutan har cikin gidajenmu muke jin harbi, yanayin da ke mu gudu don neman inda za mu samu mafaka," in ji shi.
‘Yan gudun hijirar daga wadannan yankuna sun bukaci hukumomin kasar su kawo musu dauki tare da daukar matakan da suka dace don kawo karshen rikicin kasar baki daya.