DUNIYA
2 minti karatu
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullally bayan Justin Welby ya yi murabus sakamakon wani rahoto ya gano Cocin Ingila ta yi rufa-rufa kan cin zarafin yara maza a shekarun 1970s, kuma bai sanar da hukumomi ba a lokacin da aka sanar da shi a 2013.
An naɗa Sarah Mullally mace ta farko Shugabar Cocin Ingila
Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106. / Reuters
3 Oktoba 2025

Sarah Mullally ta zama sabuwar Shugabar Cocin Ingila, wato Archbishop ta Canterbury, inda ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Cocin Ingila — inda wannan muƙamin ya samo asali tun zamanin Daular Romawa — da kuma al'ummar Anglican na duniya.

Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullaly bayan kwamitin ka dora wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Justin Welby, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar saboda wani zargi na cin zarafi, kamar yadda gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Jumma'a.

Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106.

A cikin wata sanarwa, tsohuwar ma'aikaciyar jinya ta bayyana cewa ta fahimci "babban nauyi" da ke tattare da sabon aikinta, amma ta ce tana jin "nutsuwa da amincewa ga Allah don ya taimake ni."

Firaminista Keir Starmer ya yi maraba da nadin mace ta farko da za ta rike wannan mukami. “Cocin Ingila tana da matukar muhimmanci ga wannan kasa. Coci-cocinta da majami'unta, makarantu, da kungiyoyin agaji suna cikin tsarin al'ummominmu,” in ji shi a wata sanarwa, yana mai cewa sabuwar Archbishop za ta “taka rawar gani a rayuwar kasa.”

Welby ya yi murabus bayan wani rahoto ya gano cewa Cocin Ingila ta yi rufa-rufa kan cin zarafin da ya faru a shekarun 1970s, kuma bai sanar da hukumomi ba lokacin da aka sanar da shi a 2013.

Rahoton binciken ya bayyana cewa John Smyth, lauya da ya shirya sansanonin bazara na evangelical a shekarun 1970s da 1980s, shi ne ya yi wa yara maza da matasa har 130 cin zarafi. Smyth ya mutu yana da shekaru 75 a Afirka ta Kudu a 2018 yayin da 'yan sandan Birtaniya ke bincike a kansa. Bai taba fuskantar wata tuhuma ta laifi ba.

Wannan badakala ta girgiza Birtaniya kuma ta haifar da kira kan a yi gyara a Cocin Ingila, wanda babban jagoran cocin shi ne Sarkin Ingila. Cocin Ingila tana da mambobi kusan miliyan 20, amma adadin masu zuwa coci a kai a kai an kiyasta ya kai kasa da miliyan daya, bisa ga alkaluman 2022.