Ƙasar da ke ƙarƙashin kofatonsu da alama tana girgiza yayin da garken ɓauna ke yin tururuwa zuwa kogin Chobe da ke gabashin Namibiya, wanda manyan zakuna ke bin su don farauta.
Aƙalla ɓauna 90 ne ko dai aka tattake su har suka mutu ko kuma suka nutse a cikin taɓon kogin a yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Wannan al'amari mai ban mamaki ya afku ne da asuba a ranar 23 ga Satumba a kan iyakar arewa maso-gabashin Babban Dajin Chobe na Botswana, wuri mai daɗin zama ga giwaye, raƙuman dawa, da ɓauna da dama.
A cikin 'yan shekarun nan, duk da haka, wurin shaƙatawar ya samu matsala saboda yawan mace-macen ɓauna wanda ya haifar da tambayoyi game da ɗaya daga cikin tsoffin rikicin namun dawa, tsakanin mai farauta da ake farautowa.
"Zakuna sun kori garken ɓauna daga maƙwabciyar ƙasar Botswana. Wasu dabbobin sun faɗo daga wani dutse zuwa cikin kogin wasu kuma sun tattake juna," in ji Ndeshipanda Hamunyela, kakakin ma'aikatar yawon buɗe ido ta Namibiya.
Hotunan matattun ɓauna da ke yawo a cikin kogin sun bazu a shafukan intanet, lamarin da ya sa kanun labaran duniya ke ci gaba da janyo tafka muhawara kan ko za a iya sauya dabarun kiyayewa domin daƙile waɗannan munanan tashe-tashen hankula da ke faruwa a dazuzzukan kudancin Afirka.
Matsala da ke yawan faruwa
A watan Oktoban 2023, fiye da ɓauna 100 ne suka mutu a kusan yanayi iri ɗaya lokacin da manyan zakuna masu farauta 12 suka koro su zuwa tafkin.
Shekaru biyar da suka gabata, kusan ɓauna 400 ne suka nutse a turmutsutsu guda ɗaya, kuma ana kyautata zaton zakunan da ke bin garken ne ya haddasa lamarin.
Yanayin bai iyakance ga Botswana da Namibiya kaɗai ba. A watan Agustan 2024, jami'an hukumar kula da namun daji ta Zambiya sun gano gawarwakin ɓauna 52 a bakin kogin Musa a dajin Kafue. Jami’an yankin sun tabbatar da cewa dukkan su sun mutu ne sakamakon wani turmutsitsin da aka yi.
Wani kaulin kuma shi ne na cewa mace-macen bauna a cikin turmutsutsu na bukatar ingantaccen bayani fiye da na ra’in tsira na Darwiniyanci.
Batun da ke ta yawo a kafafen sada zumunta shi ne cewa ingantaccen aikin kula da namun daji masu farauta da wadanda ake farauto wa na iya kawar da mutuwar tasu. Wasu kuma suna jayayya cewa shiga tsakani a cikin yanayin na iya haifar da cutarwa fiye da amfaarwa.
Dr Gladys Kalema-Zikusoka, likitar dabbobi 'yar Uganda, ta bayar da shawarar tsarin jira da sanya idanu a matsayin mafita.
Ta shaida wa TRT Afrika cewa "Kamar yadda abin ke damun zuciya kamar yadda ya kan bayyana a wasu lokuta, ba shi da kyau ga wadannan dabbobi idan aka samu shiga tsakani na ɗan’adam. Wani lokaci, yana da kyau a bar rayuwa ta dauki mataki da kanta. Dabbobi a kodayaushe suna saba wa. kuma suna dawo wa da adadi, ba tare da la'akari da barazanar da suke fuskanta ba."
Matakin da ba a bayyana shi
Bincike da Ƙungiyar Ƙwararrun ta ɗauka ya nuna cewa garken ɓauna na iya kare kansu daga manyan namun daji masu farautar su har ma su kashe su.
Ɓauna na ci gaba da fuskantar hatsari, suna dogaro da wari, sauti da gani don gano mafarauta. Lokacin da ƴan dabbobi suka firgita, sanarwar kar-ta-kwana na yaɗuwa da sauri ta hanyar muryoyinsu, motsin jiki da motsi na ba zata. Wannan yana haifar da martani a jere daga garken ɓaunar.
Dabbobi a faɗin duniya waɗanda masu rubutun ra'ayi a intanet da ke kawo labarai game da yanayi da kariya daga ƙasashe 67 na nahiyoyi shida, sun kawo wani bincike na kimiyya wanda ya tabbatar da cewa ba kowace ɓaune ce ke buƙatar ganin mafarauci ba kafin fara ɗaukar matakan kariya. Kallon yadda sauran ‘yan garke ke gudu kawai ya isa ya jawo tafiyarsu gaba ɗaya a lokaci guda.
Halayyar da aka saba gani
Saboda haka, mene ne ke haifar da waɗannan munanan turmutsutsu mai kisa idan dabbobi suna ankare da hatsarin da ke tafe?
Masana ilimin halittu suna kallon turmutsutsu a matsayin hanyar kariya da suka saba da ita, amma kuma mai ɗauke da mummunan sakamako. Ƙarƙashin matsin lambar namun daji masu farauta, ɓauna na tattaruwa a matsayin manya-manyan garke kuma su matsa zuwa fili don rage hatsarin kwanton-ɓauna.
Yayin da wannan ke inganta amincin bai-ɗaya, yana kuma nufin cewa lokacin da firgita ta zo, dubban kofato na iya mutuwa.
Turmutsutsu ba ko yaushe ne yake zama na rikicin shiga jirgi ba. A 2020, maziyartan dajin Kruger na Afirka ta Kudu sun kalli sama da ɓauna 100 da suka kai wa zakuna hari a matsar ruwa ta Mestel, inda suka kashe ɗaya daga cikin zakunan.
Masana sun yi imanin dole ne a dinga samun turmutsutsu kamar wanda ya faru a wannan watan a kogin Chobe.
Dr Kalema-Zikusoka ya bayyana cewa da wahala a san lokacin da ya kamata a ɗauki mataki.
"Gaskiya abu ne mai wahala a san abin da za a yi, kuma yawancin su ma na faruwa ne sakamakon ƙalubalen da sauyin yanayi ke haifarwa. Lokaci daya tilo da 'yan’adam ke buƙatar shiga tsakani su cire ko tsugunar da dabbobin shi ne idan sun shiga cikin hatsari."