1459 GMT — Karin Falasdinawa 24 da ke asibitin Gaza sun rasa rayukansu
Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin da ke Gaza ta ce a kwanaki biyu da suka gabata marasa lafiya 24 ne suka mutu a asibitin Al Shifa saboda yanke lantarki, a yayin da dakarun Isrs'ila ke ci gaba da neman maboyar Hamas.
Kakakin ma'aikatar Ashraf al Qudra ya shaida cewa "Marasa lafiya ashirin da huda a bangari daban-daban na asibitin sun mutu a awanni 48 da suka gabata saboda muhimman kayan kula da lafiya sun daina aiki sakamakon katsewar lantarki."
A ranar Litinin, ma'aikatar ta bayyana mutuwar mutane 27 da suka hada da jarirai bakwai sakamakon rashin man fetur a babban asibitin Gaza.
0933 GMT — Halin da ake ciki a Gaza 'yana matukar tayar da hankali', ba a iya kai agaji arewacin yankin — UNRWA
Abu ne mai “matukar wahala” shigar da kayan agaji arewacin Gaza kuma halin da ake ciki a can na “matukar damuwa ne,” a cewar shugaban Hukumar Bayar Da Agaji ga Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA).
Kiyasi ya nuna cewa a yanzu akwai mutum 250,000 zuwa 300,000 a arewacin Gaza, a cewar Kwamishina-Janar na UNRWA Philippe Lazzarini a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu a birnin Geneva.
“Abin takaici shi ne, tun da aka kaddamar da hare-hare ta kasa ba mu da cikakken bayani game da halin da ake ciki a arewacin yankin,” in ji shi, yana mai karawa da cewa yanzu UNRWA ba ta da wakilai a yankin.
0700 GMT — Ministan tsaron Isra'ila ya yi ikirarin kwace iko da yammacin Birnin Gaza
Sojojin Isra'ila sun kwace iko da yammacin Birnin Gaza, a cewar ministan tsaron kasar, yana mai sanar da soma "mataki na gaba" na kutsen da suke yi ta kasa.
A yayin da yake magana da sojojin Runduna ta 36 da ke kudancin Isra'ila, Yoav Gallant ya ce: "A awanni 24 da suka gabata, mun kwace iko da yammacin Birnin Gaza, kuma mun soma mataki na gaba na hare-haren da muke kaiwa ta kasa."
Ya kara da cewa: "Da zarar mun matsa kaimi a wannan yaki, hakan zai matsa lamba kan Hamas kuma za mu yi nasara wajen kawar da kayan yakinta da hedkwatarta da gine-ginen karkashin kasarta."
Hare-haren da Isra'ila ta kaddamar ta sama da ta kasa a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba sun yi sanadin kashe Falasdinawa sama da 11,000, fiye da rabinsu mata da kananan yara.
0625 GMT — Hamas ta ce ta shirya gwabza yaki mai tsawo da Isra'ila
Shugaban bangaren siyasa na Hamas ya ce kungiyar da ke Zirin Gaza ta shirta tsaf domin gwabza yaki na tsawon lokaci da sojojin Isra'ila.
A wani jawabi da aka nada kuma ya gabatar ranar Alhamis, Ismail Haniyeh ya jinjina wa Falasdinawa da kuma yadda suka hada kai wajen “wargaza sojojin Isra'ila da rage musu karfi ta kowacce fuska.”
“Idan har makiya suna so a yi yaki mai tsawo, karfinmu ya fi na makiyanmu kuma bijirewarmu ba za ta gushe ba,” yana mai nuna cewa “mayakanmu suna fafatawa a yaki da makiyanmu Yahudawa kuma za mu yi nasara,” a cewar Haniyeh.
Ya bayyana irin “nasarorin da mambobinmu suka samu a Zirin Gaza,” yana mai karawa da cewa “gwarazanmu suna fitar da mu kunya a Gaza, suna jajircewa da kuma cin galaba a kan makiyanmu da lalata ababen hawansu.”
“Duniya za ta ga lokacin da Rundunar Al-Qassam da masu taya ta aiki za su murkushe mamayar da Isra'ila ke yi a Gaza, kamar yadda suka yi shekara 18 da suka gabata.”
0550 GMT — Dubban mutane a Asibitin Al Shifa na 'kokarin kauce wa mutuwa'
Mutum fiye da 7,000 da suka hada da wadanda aka kora daga gidajensu da marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya a Asibitin Al Shifa suna "kokarin kauce wa mutuwa sakamakon rashin ruwa da abinci" saboda kawanyar da dakarun Isra'ila suka yi musu, kamar yadda ofishin watsa labarai na Gaza ya bayyana.
A wata sanarwa da ofishin ya wallafa a manhajar Telegram, ya jaddada irin mawuyacin halin da mutanen suke ciki, yana mai bayyana cewa "babu abinci da ruwa da madarar da za a bai wa jarirai a Asibitin Al Shifa."
"Bakwaini da ke fama da rashin abinci za su iya rasuwa a asibitin saboda rashin wutar lantarki, abin da ya sa aka fitar da su daga kwalaben da suke ciki," in ji sanarwar.
Ofishin ya bayyana "mawuyacin halin da ake ciki a Asibitin Al Shifa, inda mutum akalla 650 suke jiyya da kuma mutum 7,000 da aka kora daga gidajensu suke samun mafaka."
Ma'aikatan kiwon lafiya da majiyyata da mutanen da aka raba da gidajensu suna kokarin kauce wa mutuwa saboda rashin "abubuwan bukatu na rayuwa."
Sanarwar ta kara da cewa "dakarun Isra'ila sun lalata dukkan ababen hawa da ke cikin asibitin sannan sun hana ma'aikata da majiyyata fita daga cikinsa."