Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ƙaryata ikirarin da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya yi cewa ƙungiyar Boko Haram ta taɓa naɗa ubangidansa, Buhari a matsayin wanda zai shiga tsakani a tattaunawar sulhu da Gwamnatin Tarayya.
Shehu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a mai taken “Boko Haram ba ta taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakani ba.”
Kalaman Garba Shehu sun biyo bayan jawabin da Jonathan ya yi yayin taron ƙaddamar da littafin Scars, wanda tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta. A wajen taron, Jonathan ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun taɓa naɗa Buhari a matsayin mutumin da suke so ya jagoranci tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu da gwamnati.
Jonathan ya ce, “Ɗaya daga cikin kwamitin da muka kafa a lokacin, Boko Haram ta zaɓi Buhari ya jagoranci tawagarsu don yin sulhu da gwamnati.
“Sai na yi zaton idan suka zaɓi Buhari ya wakilce su a tattaunawa da kwamiti na gwamnati, to da zarar Buhari ya hau mulki, hakan zai iya zama hanya mafi sauƙi ta shawo kansu su mika makamai. Amma har yanzu matsalar na nan.”
A martaninsa, Shehu ya ce Jonathan ya “fara yada ƙarya tun kafin zaɓen 2027.”
Ya ce, “Muhammad Yusuf ko Abubakar Shekau, jagororin ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram waɗanda dukansu sun, ba su taɓa naɗa Muhammadu Buhari a irin wannan matsayi ba (ya wakilce su).
“Bugu da ƙari, Shekau ya sha caccakar Buhari da barazanar kashe shi, saboda tunaninsu da akidunsu sun saba wa juna.”
Shehu ya tunatar da cewa Buhari ya taɓa tsallake rijiya da baya daga hari na bam da Boko Haram ta kai masa a Kaduna a shekarar 2014, wanda ya jikkata wasu daga cikin ‘yan tawagarsa.
Ya kuma bayyana cewa ruɗanin ya samo asali ne daga wani taron manema labarai da wani bangare na kungiyar Boko Haram, ƙarƙashin jagorancin Abu Mohammed Ibn Abdulaziz, ya gudanar a Maiduguri a shekarar 2012, inda ya ambaci Buhari da wasu shugabannin Arewa a matsayin masu yiwuwar shiga tsakani.
“Shugabannin a lokacin sun yi ta sukar Abdulaziz inda suke cewa ba da yawun shugabansu ba Abubakar Shekau,” in ji Shehu.
A wancan lokacin, Buhari da kansa ya musanta sanin wani abu game da lamarin. Shehu ya ambaci tsohon Sakataran Jam’iyyar CPC, Buba Galadima, yana cewa:
“Har zuwa ƙarfe 10 na dare jiya lokacin da na yi magana da shi, ya ce ma bai ji labarin ba… tun da babu wanda ya tuntube shi kai tsaye, ba zai yi magana da ‘yan jarida ba.”
Lamarin ya zama wata babbar matsalar siyasa a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2015, inda Rotimi Fashekun, tsohon mai magana da yawun CPC (wanda yanzu ya rasu), ya zargi gwamnatin PDP ta Jonathan da amfani da wannan jita-jita domin neman wata mafita ta siyasa.