Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ƙara ƙaimi tare da hadin-gwiwa da hukumomin tarayya na inganta matakan tsaro a magudanan ruwa domin hana sake afkuwar irin wannan bala’i.
Ya yi kira ga jama’a a yankunan da ke gaɓar kogi da su ba da fifikon tsaro a ko da yaushe ta hanyar guje wa wuce gona da iri, da kuma amfani da rigar kariya da sauran matakan kariya a duk lokacin da suke tafiya ta ruwa.
Hatsarin kwale-kwale ya zama ruwan dare a Nijeriya, inda ake yawan samun asarar rayuka saboda hakan, musamman a yankunan da ke bakin koguna.