Shekaru biyu na kisan kiyashin Isra’ila a Gaza: Yadda Amurka ke kare Netanyahu daga tuhuma
SIYASA
7 minti karatu
Shekaru biyu na kisan kiyashin Isra’ila a Gaza: Yadda Amurka ke kare Netanyahu daga tuhumaIyakokin Falasdinu na cikin mummunan yanayi inda aka kashe dubunnan mutane, yayin datallafin sojin Amurka da hawa kujerar naki a MDD na kare shugabannin Isra’ila daga tuhumar kasa da kasa.
US has blocked Gaza ceasefire with a record sixth vetos in two years, shielding Israel from UN action. (Photo: AFP, AA, Reuters) / Public domain
7 Oktoba 2025

Shekaru biyu kenan tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba a matsayin martani ga abin da ta bayyana da hare-haren Isra'ila na kullum kan Masallacin Kudus, da tashin hankalin 'yan kama-wuri-zauna a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ke mamaya da kuma mayar da batun Falasdinu kan teburin tattaunawa.

Martanin na ba zata da harin sojojin Isra'ila cikin bacin rai, tare da Umarnin Hannibal mai cike da ce-ce ku-ce, sun yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1,200, wadanda yawancinsu sojojin Isra'ila ne da farar hula.

Daga baya, kisan gillar da Isra'ila ta yi ya sauya Gaza - wanda Isra'ila ta yi wa kawanya ta tudu, teku da iska tun 2005 - zuwa wani wuri mai muni, wanda jama'ar duniya suka shaida.

Yankin da aka yi wa kawanya ya shiga tsaka mai wuya, an lalata kayan more rayuwa da ke yankin, sannan an rusa rayuwar fararen hula. Ana tsammanin adadin wadanda suka mutu ya haura wanda ake sanarwa.

A hukumance Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 67,000 wadanda yawancin su mata da kananan yara ne. Ana kyautata zaton adadin wadanda suka mutu ya zarce haka.

Kotun kasa da kasa, babbar hukumar shari'a ta Majalisar Dinkin Duniya, ta gano cewa ayyukan Isra'ila na iya zama kisan ƙare-dangi, yayin da kungiyar malamai masu sanya idanu kan kisan kiyashi ta kasa da kasa, babbar kungiyar malaman nazarin kisan kare dangi ta duniya, ta bayyana a hukumance cewa Isra'ila ta aikata kisan kiyashi a Gaza.

Rahoton baya bayan nan na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma tabbatar da cewa Isra’ila na yi wa Falasdinawa kisan kiyashi a Gaza.

Tuni dai kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa.

Hawa kujerar naki sau shiga don kare Isra’ila

A tsawon lokacin da bala'o’i ke afka wa Falasdinawa, Amurka ta dinga goyon bayan Isra'ila.

Masu suka na ce wa yayin da jami'ai a Washington ke yawan nuna damuwa game da halin da ake ciki a Gaza, waɗannan kalmomi ba a aiki da su don takaita samar da makamai zuwa Tel Aviv ba.

A Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Amurka ta yi amfani damar hawa kujerar naki har sau shida tun daga watan Oktoban 2023 don toshe kudurori da ke da nufin kawo karshen kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza ko kuma tabbatar da kai agajin jin kai Gaza.

Hawa kujerar naki na baya bayan nan ya afku ne a watan Satumban 2025, lokacin da Washington ta yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita bude wuta nan take. Kowane hawa dokin naki ya haifar da sukar cewa ana kare Isra'ila ne daga fuskantar tuhuma.

Wannan garkuwar diflomasiyya ta taimaka, wajen mayar da hare-haren da Firaministan Isra'ila Netanyahu kai wa a Gaza ba wani abu ba, kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana. Manufofinsa sun hada da yakin basasa a birane, korar jama'a, da ruguza dukkan unguwanni.

Tun daga Oktoban 2023, taimakon soji da Amurka ke bi wa Isra'ila ya kai aƙalla dala biliyan 21. Tallafin ya shafi alburusai, harsashai, da kuma kyan kariya na makamai masu linzami da ke ci gaba da dabbaka kisan kare dangin.

A shekarar da ta gabata, Washington ta amince da wani gagarumin cinikin makamai da suka hada da jiragen yaki na zamani da kuma bama-bamai masu sarrafa kansu, kudin su ya zama sama da dala biliyan 3.8 na shekara-shekara da aka amince da shi karkashin yarjejeniyar dogon wa’adi.

A wannan lokacin, karancin abinci ya shafi dukkan mazauna Gaza sama da miliyan biyu, inda kusan rabin al'ummar kasar ke fuskantar barazanar yunwa da rashin abinci mai gina jiki.

Yayin da asibitoci ke kokawa da matsanancin karancin jini, insulin, da magunguna, suna barin wadanda suka jikkata ba tare da kulawa ba, girman bala’in ya kusan makantar da mutum ga abubuwan da suka faru a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Makamai na ci gaba da zuwa

A karshen watan Janairun 2024, an kashe Hind Rajab mai shekaru biyar a garin Gaza bayan da sojojin Isra'ila suka harba daruruwan harsasai kan motar iyayenta. Ta nemi agaji ta wayar tarho daga Kungiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Red Crescent, zane a gefen gawarwakin 'yan uwanta. An kuma gano an kashe masu aikin ceto da aka aika domin nemo ta.

Kwararrun Majalisar Dinkin Duniya sun kira lamarin da yiwuwar zama laifin yaki, wanda ke nuni da mafi munin salon kai hari ga farar hula da Isra'ila ke yi.

Makonni kadan bayan haka, a ranar 29 ga watan Fabrairu, sojojin Isra'ila sun bude wuta kan jama'ar da suka taru a kusa da motocin agaji a arewacin Gaza, inda suka kashe akalla mutane 118, tare da jikkata sama da 760.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana lamarin da kisan kiyashi tare da danganta shi da amfani da yunwa da Isra'ila ke yi a matsayin makamin yaki.

Lamarin ya kara munana a watan Afrilu, lokacin da wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan ayarin motocin cin abinci na Duniya, ya kashe ma'aikatan agaji na kasa da kasa da dama, ciki har da 'yan kasashen Amurka, Birtaniya, da Australia.

Shugabannin kasashen duniya sun yi Allah wadai da harin da cewa ya saba wa dokokin kasa da kasa, lamarin da ya tilasta wa kungiyoyin agaji da dama dakatar da ayyukansu a yankin da aka yi wa kawanya.

David Gibbs, sanannen marubuci kuma farfesa a fannin tarihi, ya ce: "Matsalar mutane da yawa ita ce ƙoƙarin kare gagarumin tallafin tattalin arziki da na soja da Amurka ke ba Isra'ila, wanda mai biyan haraji na Amurka ke ba da tallafi, kuma hakan yake ci gaba da gudana tun farkon shekarun 1970. Wannan ya kasance abu ya zama mai wahalar kare wa, la'akari da cewa Isra'ila kasa ce mai yawan samun kudin shiga, kuma tana amfani da kuɗin don ba da damar mamaye Gabar Yamma da Zirin Gaza ba bisa ka'ida ba."

Duk da irin wannan sukar, lafin mika makaman yana fadada.

A watan Agustan 2024, Washington ta amince da sayar da sabbin jiragen yaki samfurin F-15IA har guda 50 daga Boeing, da inganta jiragen da ake da su, da dubunnan makamai masu linzami na AIM-120 AMRAAM.

A karshen wannan shekarar, Isra'ila ta kuma samu fiye da tankokin yaki 32,000, bama-bamai 50,000, da dimbin manyan motoci da tirelolin tankokin yaki.

Amurka ta bayar da izinin canja wurin gaggawa na JDAMs, makamai masu linzami, da kuma Caterpillar D9 bulldozer da ake amfani da su a ayyukan Gaza.

Sauyin tunanin jama’a

Amma duk da haka halayen jama'a a cikin Amurka sun sauya sosai a cikin shekaru biyu da fara yaƙin.

Tausayi ga Isra'ila, da ake bayyana shi a fili a cikin al'amuran siyasa, ya ɓace, musamman a tsakanin matasa Amurkawa da 'yan Democrat.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kamfanin Gallup ya gudanar a watan Agustan 2025 ta gano cewa kashi 32 cikin 100 na Amurkawa ne kawai suka amince da ayyukan Isra'ila a Gaza, kasa daga kashi 50 cikin 100 a karshen shekarar 2023. Kashi 60 cikin 100 dai ba su amince da hakan ba.

Wani bincike na daban na New York Times/Siena da aka yi daga watan Satumban 2025 ya gano cewa kashi 53 cikin 100 na waɗanda suka amsa tambayoyin suna adawa da ƙarin taimako ga Isra'ila, inda kashi 40 cikin ɗari kuma na da ra’ayin Isra'ila na kai hari kan farar hula da gangan.

Masanin manufofin kasashen ketare na Amurka David Levine ya ce "Munanan abubuwan da ake gani na mahimmanci."

Canjin ya zama babu makawa a tsakanin wadanda ke kasa da shekaru 35. Sabbin bayanan Pew sun gano cewa kashi 70 cikin 100 na matasan Amurkawa suna da ra'ayi mara kyau game da Isra'ila, yayin da fiye da rabin su ke tausayawa Falasdinawa.

Binciken Brookings  ya lura da irin wannan tsari, tare da ɓacin rai ya yadu a tsakanin ‘yan jam'iyyu.

Gibbs ya ce "Yawancin matasan 'yan jam'iyyar Republican suna adawa da ajandar goyon bayan Isra'ila, musamman ma batun tallafi."

“Mutanen da ke bangarorin biyu na siyasa za su iya gani da idanunsu munanan bidiyon abin da Isra'ila ke yi a Gaza."

Yanzu dai idanuwa sun karkata kan tattaunawa game da shirin Trump na kawo karshen kisan kiyashi a Gaza.

Yayin da kungiyar Hamas ta amince da wasu sassa na yarjejeniyar, Isra’ila da ta yi wa yarjejeniyar tsagaita wuta a baya zagon kasa, na ci gaba da kai hare-hare kan Falasdinawa da makwaftansu, duk da umarnin Trump na dakatar da kai hare-haren.