AFIRKA
2 minti karatu
Ayyukan da sojojin Nijar suke yi a yankin Tillaberi sun fara tasiri: Shugaba Tiani
Shugaba Tiani ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara Jihar Tilleberi inda ya yi rangadin dakarun da ke jihar wadda ke fama da matsalar tsaro.
Ayyukan da sojojin Nijar suke yi a yankin Tillaberi sun fara tasiri: Shugaba Tiani
Shugaban Nijar ya kai ziyarar aiki jihar Toilleberi da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda / ANP
6 Oktoba 2025

Shugaban ƙasar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya shaida wa jami’an tsaron runduna ta 9 mai suna “Operation Niya,” cewa “ayyukan da kuke yi kullum sun fara tasiri.”

Shugaba Tiani ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara Jihar Tilleberi inda ya yi rangadin dakarun da ke jihar wadda ke fama da matsalar tsaro.

Janar Abdourahamane Tiani ya taya dakarun tsaron murna game da gagaruman ƙoƙarin da suke yi a ko wace rana kan tabbatar da yanayi na tsaro domin amfanin dukkan al’umma.

 "Aikin da kuke yi a ko wace rana ya fara tasiri," kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ambato shugaban ƙasar yana cewa.

Shugaban ya jaddada cewa shi ya ga irin "jajircewa [ta dakarun] da kuma tasirinta,” yana mai yabawa da ayyukan dakarun operation Niya da kuma sadaukarwarsu.

 Shugaban ya kuma tabbatar wa dakarun cewa ƙasar baki ɗaya tana sane da ƙoƙarinsu.

“Domin ci-gaba da kuma samun nasarar kawo ƙarshen wannan rashin tsaron, gwamnati tana iya ƙoƙarinta, Muna sane da girman ƙasarmu da kuma ƙwarewar ko wane fagen daga,” in ji shugaban.

Shugaban ya ƙara da cewa abin da ya gani da idonsa ya ƙarfafa matakinsa na ƙara ɗaukar ƙarin jami’an tsaro domin iya cike dukkan yankin nan gaba.

 “Daukar jami’an ba shi ne kawai ba, dole mu ba su horo da kuma kayan aiki ta yadda za su iya tunkarar barazana. Idan ina maganar kayayyakin aikin wannan ya haɗa da na ƙasa da na sama,” in ji shugaban

Shugaban da ya samu tarbar malama da sarakunan  gargajiya da mutanen jihar Tilleberi, yana ziyara ne a yankin domin ƙarfafa wa dakarun da ke yankin da ke fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Kamfanin dillancin labran ƙasar ta ruwaito cewa shugaban ƙasar ya fara ziyayar aiki a jihar Tilleberin ne tun ranar 4 ga watan Oktoba kuma ziyarar ta ci gaba ranar Lahadi 5 ga watan Oktoba.