AFIRKA
2 minti karatu
ICC ta tuhumi shugaban ‘yan bindiga na Sudan Ali Kushayb da laifukan keta hakkin bil’adama
Tuhumar ce hukuncin ICC na farko da ya shafi rikicin Darfur kuma ana sa rai zai zama misalin yin adalci a ɗaya daga cikin rikice-rikicen jinƙai mafiya daɗewa a Afirka.
ICC ta tuhumi shugaban ‘yan bindiga na Sudan Ali Kushayb da laifukan keta hakkin bil’adama
Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman ya halarci zaman kotun ta ta ICC a yayin da ma shari'a ya bayyana hukuncin da aka yanke amsa kan laifukan yaki. / Reuters
7 Oktoba 2025

Kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa a ranar Litinin ta samu wani babban jagoran mayakan sa-kai na Sudan da laifi bayan an kai ƙararsa kan zargin aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama a lokacin kai munanan hare-hare a yankin Darfur.

An tuhumi Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da nom de guerre Ali Kushayb da laifuka da dama da suka haɗa da fyaɗe, kisa da azabtarwa da aka yi a tsakanin watan Agustan 2003 zuwa Afrilun 2004.

Binciken da kotun ta ICC ta yi ya gano cewa Kushayb ya jagoranci kai hare-hare kan fararen-hula a lokacin yaƙin Darfur, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban ɗaruruwan mutane tare da raba miliyoyi da matsugunansu. An mayar da shi hannun kotun ICC a ranar 9 ga watan Yunin 2020 bayan ya miƙa kansa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma ya a karon farko ya bayyana a gaban kotu a ranar 15 ga Yunin 2020.

Bayan sauraren ƙarar a watan Mayun 2021, kotun ta tabbatar da laifuka 31 na laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama tare da gurfanar da Kushayb a gabanta.

An fara zaman shari'ar a hukumance a ranar 5 ga Afrilun 2022, tare da mutane 56 da za su bayar da shaida yayin shari'ar.

Wakilan waɗanda abin ya shafa su ma sun gabatar da ra'ayoyinsu, kuma masu kariya sun kira shaidu 18 kafin a saurari ƙarar a watan Disamban 2024.

Tuhumar ce hukuncin ICC na farko da ya shafi rikicin Darfur kuma ana sa rai zai zama misalin yin adalci a ɗaya daga cikin rikice-rikicen jinƙai mafiya daɗewa a Afirka.