Aƙalla fararen-hula shida ne aka kashe yayin da aka jikkata 24 a wani harin na manyan bindigogi da aka kai wani sansanin ‘yan gudun hijira a Al Fasher da ke Yammacin Sudan, kamar yadda wani kwamitin jinƙai na ƙasar ya bayyana, inda ya zargi dakarun RSF da kai harin.
“A yau, RSF ta kai hari kan jerin kicin na abinci a Al Fasher, inda ta kashe fararen-hula shida kuma ta jikkata sama da wasu 24,” in ji kwamitin da ke jagorantar gwagwarmaya a Al Fasher a wata sanarwar da ta fitar ranar Talata.
“Har kicin ɗin da ke kasancewa mafaka ga talakawa da masu jin yunwa ma bai tsira daga harin RSF ba. An lalata tukwane kuma aka baza abinci a ƙasa, tamkar ƙaddamar da yaƙi kan masu rauni da masu jin yunwa ne,” a cewar sanarwar.
Jerin kicin ɗin – wanda ake kira Takaya – wuri ne na al’umma wanda ke ba da abinci ga mazauna wurin da waɗanda aka raba da muhallansu a Al Fasher da ma wasu wuraren da ake yaƙi wanda ‘yan sa-kai ne ke tafiyar da shi da tallafin masu taimaka wa jama’a da ƙungiyoyin ba da agaji.
Gwamnan yankin Darfur Minni Arko Minnawi ya ce kai hari kan ɗaya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira a Al Fasher da mayaƙan rundunar RSF suka yi ya nuna “wani sabon laifi da ya ƙaru kan tarihinta na zubda jinin fararen hula mara makamai.”