Zanga-zangar da matasa ke jagoranta mai neman a inganta ilimi da kiwon lafiya a ƙasar Maroko ta kai ga arangama da jami’an tsaro, inda aka shiga kwana na huɗu a jere na zanga-zanga a faɗin ƙasar.
Ana tsara zanga-zangar ne ta intanet inda ake amfani da kafafen TikTok da Instagram da kuma manhajar gem ta intanet ta Discord.
A biranen kudancin ƙasar na Tiznit da Inzegane da Ait Amira da kuma biranen gabashin ƙasar na Oujda da Temara kusa da babban birnin ƙasa Rabat, ɗaruruwan matasa masu zanga-zanga sun yi ta jifan dakarun tsaro da ke neman tarwatsa su, kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar da shaidun gani da ido suka bayyana.
A Ait Amira, da ke da nisan kilomita 560 kudu da Rabat, masu zanga-zanga sun kayar tare da ƙona motocin jami’an tsaro da kuma ƙona wani banki, kamar yadda bidiyon da aka wallafa shafukan sada zumunta ya nuna.
A Inzegane, bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna masu zanga-zanga sanye da takunkumin rufe fuska sun ƙona banki yayin da wasu ke arangama da ‘yan sanda da ke watsa ruwan zafi.
An ƙona wasu motoci, da kuma wani gungun masu zanga-zanga da suka yi ƙoƙarin kutsa cikin wani babban kanti, in ji shaidu da kuma bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta.
‘Ƙarshen cin hanci da rashawa’
A can Tiznit da ke kudancin kuma gomman masu zanga-zanga sun wurga duwatsu kan jami’an tsaro yayin da suke ƙoƙarin tarwatsa jerin gwanon, kamar yadda shaid suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.
Masu zanga-zanga sun rera take iri-iri ciki har da “Mutane na son a kawo ƙarshen cin hnaci da rashawa,” in ji su.
A Oujda, wani mai zanga-zanga ya ji rauni mai muni bayan wata motar jami’an tsaro ta kaɗe shi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar MAP ya ruwaito.
A birnin Rabat, ‘yan sanda sun kama gomman matasa yayin da suka fara rera take a wata unguwa mai tarin jama’a, kamar yadda wani shaidan Reuters ya bayyana.
Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Maroko (AMDH) an ba da belin matasa 37, zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Hakim Saikuk, shugaban ɓangaren AMDH a Rabat, ya yi Allah wadai da kamen a matsayin wani abu da ya saɓa wa tsarin mulki.
A Casablanca, msu zanga-zanga 24 da suka tare babban titi ranar Lahadi sun kasance a ƙarƙashin bincike na shari’a, kamar yadda mai gabatar da ƙara na gwamnati ya bayyana.
Haɗaka ta gwamnati ta fitar da wata sanarwa ranar Talata inda ta bayyana yardarta da shiga tattaunawa da matasan "cikin hukumomi da kuma wurare na gwamnati domin a a samar da mafita na gaskiya".
Ta kuma yaba wa abin da ta kira "martanin mai daidaito na jami’an tsaro bisa tsare-tsaren doka."
Ma’aikatar tsaron cikin gida ba ta yi tsokaci kan lamarin nan take ba.