Ra'ayi
SIYASA
5 minti karatu
Swahili ne mafita ga Gabashin Afirka ba Faransanci ba
Harshe ne ruhin al’umma. Fifita Faransanci a kan Swahili a Gabashin Afirka na raunata al’adu da dangantakar yanki.
Swahili ne mafita ga Gabashin Afirka ba Faransanci ba
Swahili babban harshen gabashin Afirka da sama da mutane miliyan 200 ke magana da shi. / Others
9 Oktoba 2025

Daga Isaac Bagaya

A cikin kasar da ke da bambancin harasa kamar Uganda, inda ake magana da harsuna sama da 40 a duk faɗin ƙasar, zaɓin yaren da za a haɓaka zai iya haɗe kai ko wargaza makomar ƙasar.

Amma duk da haka, ɗan takarar shugaban ƙasa a 2026 Mubarak Munyagwa ya haifar da ce-ce-ku-ce saboda bayar da shawarar cire Swahili daga jerin harsunan ƙasar tare da maye gurbinsa da Faransanci.

Alƙawarin nasa, wanda aka shirya a matsayin mataki na cigaban zamani, ya yi watsi da al'adu da kuma wulaƙanta asali da tushen Uganda, da kuma rawar da take takawa ta tattalin arziki a cikin Ƙungiyar Ƙasashen Gabashin Afirka (EAC).

A wajen Uganda, wadda ke matsayin cibiyar haɗin gwiwar yankin, Swahili ba harshe ba ne kawai; wata ƙofa ce ta cigaban tattalin arziki da zaman lafiya, abin da ya sa sha'awar amfani da Faransanci ta zama kamar maras muhimmanci idan aka kwatanta su.

Ta fuskar tattalin arziki, Swahili ba makawa ne ana bukatar sa. Uganda, wadda ke da muhimmanci ta mamaye harkokin bunƙasar tattalin arzikin Gabashin Afirka, tana da alaƙa sosai da kungiyar EAC, wadda ta haɗa da Kenya, da Tanzania, da Rwanda, da Burundi, da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Harshe mafi karfi a yankin

Swahili shi ne harshen da ya fi karfi a nan, wanda sama da mutane miliyan 200 ke magana da shi a duk faɗin yankin. Shi ne harshen kasuwannin da ke cike da cunkoson jama'a a Nairobi, yarjejeniyoyin diflomasiyya a Arusha, da yankunan cinikayyar kan iyaka da ke fitar da kofi, da zinare, da kuma noma na Uganda.

Ƙwarewa wajen magana da harshen Swahili ba kawai sauƙaƙa kasuwanci ke yi ba; yana buɗe hanyoyin zuba hannun jari, yawon shakatawa, da ayyukan yi.

Ƙoƙarin Uganda na mayar da Swahili darasi a makarantu tun 1992 ya nuna hakan, ko da yake an ci gaba da nuna tirjiya—har zuwa kwanan nan, yayin da watsi da shi ke nufin nuna wariya da keɓancewa.

Sabanin haka, Faransanci ba shi da tasiri mai amfani a wannan yanki. Yayin da yake zama harshen hukuma a yayin tarukan kasa da kasa da sassan Afirka ta Tsakiya, ciki har da a DRC da Rwanda.

Birtaniya ce ta yi wa Uganda mulkin mallaka, ba Faransa ba; Turanci ya riga ya zama ƙofarmu ta isa ga duniya. Tilasta Faransanci kan 'yan Uganda zai nisantar da su daga juna ba wai haɗe kawunansu ba, wanda zai tilasta musu su haddace harshen da ba shi da alaƙa da rayuwarsu ta yau da kullun da maƙwabtansu.

Swahili, ya samo asali daga harsunan Bantu da miliyoyin mutane ke magana da shi a Uganda—daga Luganda zuwa Runyankole—ya yi nisa sosai, yana dogara da kalmomi da nahawu waɗanda mutanen gida suke fahimta cikin sauƙi.

Ba arashi ba ne cewa Swahili yana bunƙasa a gundumomin Uganda kamar Kiryandongo, inda harshe ne na asali, ko kuma a kan iyakoki kamar Bwera, inda yake jin shi yaren gida ne ma.

Mai haɗa kawuna

Bayan kasuwanci, Swahili yana ɗinke al'adun Gabashin Afirka waje guda. Ba kalmomi kawai ba; jirgin ruwa ne na labarai, kade-kade, da fasaha wanda ya ƙetare iyakokin kasa.

Daga waƙar Shaaban Robert zuwa waƙoƙin Bongo Flava, Swahili yana haɓaka bambance-bambancen al'adun Uganda, da haɓaka yawon shakatawa da haɗin kai na zamantakewa.

A ƙasar da ƙabilanci ya rarraba ta, Swahili na haɗe tsakanin kabilu da yankuna. Hatta shugaba Yoweri Museveni ya amince da shi, yana mai bayyana yiwuwar sa na zama "harshen duniya mai ƙarfi" ga kasashe mambobin EAC.

Ture shi gefe guda tare da daukar Faransanci zai wargaza wannan haɗin kai, da mayar da Uganda saniyar ware a daidai lokacin da haɗin gwiwar yanki ke da mahimmanci.

Yayin da EAC ta amince da Swahili a matsayin yaren hukuma tare da Ingilishi da Faransanci, ɗaukaka Faransanci fiye da Swahili na da hatsarin mayar da Uganda saniyar ware.

Faransanci na iya buɗe kofofin zuwa Paris ko Brussels, amma Swahili shi ne mabuɗin Dar es Salaam da Gabashin Kinshasa, inda yake da karfi sosai.

Abubuwan haɗin kai na duniya, amma mahimmancin yanki shi ne mafi a’ala. Swahili yana ba wa 'yan Uganda damar samun ayyukan yi a cikin manyan tafkunan noma, ayyukan wanzar da zaman lafiya inda yaren yake da ƙarfi, ko wajen bunƙasa kasuwancin Afirka a ƙarƙashin yankin Kasuwancin Nahiyar Afirka Ba Tare da Shinge ba.

Ruhin jama’a

Shawarar Munyagwa ba kawai ba ta da amfani ba ne; koma baya ce. Uganda ta daɗe tana kokawa don rungumar Swahili baki ɗaya saboda alaƙar tarihi da gwamnatocin baya, amma sauye-sauyen manhajoji na baya-bayan nan sun nuna za a kai ga gaci.

Yin watsi da Swahili yanzu zai lalata cigaban shekaru da dama, zai raba al'umma, da kuma kawo cikas ga cigaban tattalin arziki.

Masu tsara manufofi za su fi amfani da arzikin ƙasa don horar da malamai da haɓaka kafofin watsa labarai don ƙarfafa gwiwar koyo da koyar da Swahili.

Kamar yadda Firaminista Robinah Nabbanja ya tabbatar, Swahili "yana da matukar muhimmanci wajen samar da fahimtar haɗin kai a Gabashin Afirka."

A ƙarshe, harshe ba ƙaramin abu ba ne - ruhin mutane ne. Ta hanyar fifita Faransanci akan Swahili, Munyagwa na yin kasadar sayar da ruhin Uganda da Gabashin Afirka don sayen wani abin rufe fuska na ƙasa da ƙasa.

Cin amanar al'adunmu ne, da makwabtanmu, da makomarmu. Uganda ta cancanci shugabannin da za su jagoranci harshen ci gaba - kuma wannan harshen Swahili ne, ba Faransanci ba.

Marubucin, Ishak Bagaya  malami ne mai koyar da harshen Swahili a Uganda.

Togaciya: Ba lallai ra’ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra’yoyin dab’i na TRT Afrika ba.