Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwato yankuna da dama da ke ƙarƙashin mayaƙan rundunar ko-ta-kwata ta Rapid Support Forces (RSF) a El-Fasher, babban birnin Jihar North Darfur da ke yammacin Sudan.
Wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce dakarunta sun kai farmaki a “wurare daban-daban” da ke hannun mayaƙan RSF a El-Fasher inda suka sanya su yin asarar dakaru da kayayyakin aiki.
Kazalika rundunar sojin ta ce dakarun nata sun ƙwace motocin yaƙi da dama, ko da yake ba ta faɗi adadinsu ba, amma ta ƙara da cewa sun lalata motocin yaƙi shida, ciki har da motoci masu sulke.
A cewar rundunar sojin, mayaƙan RSF sun ƙaddamar da hari a kudacin El-Fasher, amma sojojin gwamnati sun daƙile harin sannan suka haddasa musu asara mai yawa.
Kawo yanzu rundunar RSF ba ta yi raddi game da sanarwar sojojin Sudan ba.
An yi wa El-Fasher ƙawanya
Dakarun RSF sun yi wa yankin El-Fasher ƙawanya tun ranar 10 ga watan Mayun 2024, duk da gargaɗi da ƙasashen duniya suka yi game da hatsarin yi wa birnin ƙawanya, wanda ya kasance cibiyar ayyukan agaji ga jihohi biyar da ke Darfur.
El-Fasher yanki ne da ke da matuƙar muhimmanci, don haka ƙwacewar da dakarun soji suka yi masa za ta kasance wani babban koma-baya ga dakarun RSF. Dakarun na RSF sun rasa wurare da dama tun bayan da rundunar sojin Sudan ta fatattake su daga Khartoum a watan Agusta.