AFIRKA
2 minti karatu
Jami'an tsaron Nijar sun kama hodar ibilis ta CFA biliyan 2.6
Jami'an tsaron sun kama wani direban mota ɗan Nijeriya ɗauke da sunƙi 47 na hodar ibilis da nauyinsu ya kai kilo 51.7, waɗanda ya ɗauko tun daga Ghana zai kai su Yamai.
Jami'an tsaron Nijar sun kama hodar ibilis ta CFA biliyan 2.6
An cafke direban motar, wanda ɗan Nijeriya ne mai shekaru kusan talatin, tsohon ma’aikacin ne na kamfanin sufuri a birnin Yamai. / TRT Afrika Hausa
3 Oktoba 2025

Haɗakar Jami’an Hukumar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi (OCRTIS) tare da Dakarun Tsaro na Nijar sun yi nasarar daƙile wata babbar hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, inda aka cafke wata babbar mota da ke ɗauke da hodar ibilis da kuɗinta ya kai CFA biliyan 2.6.

Bisa sahihan bayanan sirri, jami’an tsaro sun tare wata Toyota ƙirar Highlander mai launin baƙi da aka saka mata na’urar GPS, wadda ‘yan damfara suka tanada domin bibiyar hanya, amma ita ce ta taimaka wajen kamo su. A cikin motar, jami’an tsaro sun gano sunƙi 47 na hodar ibilis, waɗanda nauyinsu ya kai kilo 51.7.

An cafke direban motar, wanda ɗan Nijeriya ne mai shekaru kusan talatin, tsohon ma’aikacin ne na kamfanin sufuri a birnin Yamai. Binciken da hukumomi suka gudanar a kansa ya nuna cewa yana yi wa wata babbar dabar safarar miyagun ƙwayoyi.

Daga Ghana Zuwa Maghreb: Hanyar Safarar Kwayoyi

Binciken wucin-gadi ya nuna girman wannan harkallar safarar ta ƙwayoyi. An fito da hodar ne daga Accra da ke Ghana, inda aka tafi da ita Yamai. An shirya sake mata mazubi a can Yamai ɗin kafin a tafi da ita zuwa Agadez.  ana nufin kai shi Niamey inda za a sake kunshe shi kafin a tura shi ta Agadez zuwa Maghreb, inda daga nan zai nufi kasuwannin Turai.

Wannan hanya ta shahara ga jami’an tsaro, sai dai ba a cika samun irin wannan ƙazamin lamarin ba.

Ƙarin kame da ƙwace kadarori

Bayan cafke motar a Gaya, jami’an tsaro sun gudanar da karin samame a Yamai, inda aka kama wasu mutum biyu.

A wuraren bincike, an gano wata babbar hanyar halasta kudaden safarar ta hanyar saye da mallakar kadarori. An kwace gidaje hudu na alfarma da wasu motoci su ma na alfarmna da kuma takardun mallakar gonaki da gine-gine da dama.

Haka kuma, an sanya makaranta mallakar daya daga cikin wadanda ake zargi cikin bincike, abin da ya nuna yadda suka zuba jari a harkokin ilimi da dukiya domin ɓoye kudaden haram.