AFIRKA
2 minti karatu
An yanke wa wani mutum hukuncin kisa kan zagin shugaban ƙasar Tunisia a Facebook
Lauyan wanda aka yanke wa hukuncin ya ce mutumin ba shi da wani cikakken ilimi sannan abubuwan da ya rinƙa wallafawa a Facebook akasari kwafo su ya rinƙa yi daga wasu shafuka domin jawo hankalin gwamnati kan mawuyacin halin da jama'ar ƙasa ke ciki.
An yanke wa wani mutum hukuncin kisa kan zagin shugaban ƙasar Tunisia a Facebook
Shugaban Tunisiya Kais Saied / AP
4 Oktoba 2025

Wata kotu a Tunisiya ta yanke hukuncin kisa kan wani mutum mai shekaru 51 saboda irin abubuwan da ya rinƙa wallafa a Facebook waɗanda ake gani a matsayin cin mutuncin Shugaba Kais Saied kuma suna barazana ga tsaron ƙasa, in ji lauyansa a ranar Juma’a.

An yanke wa wanda ake zargin, wanda ba a bayyana sunansa ba, hukunci ranar Laraba bisa tuhume-tuhume uku: yunkurin kifar da gwamnati, zagin shugaban ƙasa, da kuma yaɗa bayanan ƙarya ta yanar gizo.

Alkalai sun ce wallafe-wallafen sun tayar da tarzoma da rikici, kuma sun saɓa wa dokar laifuka ta Tunisiya da kuma dokar laifukan yanar gizo ta 2022, wato Decree 54. Wannan hukuncin shi ne irinsa na farko a Tunisiya.

Duk da cewa akwai hukuncin kisa a cikin dokokin laifuka na Tunisiya, kuma kotunan farar hula suna yanke irin wannan hukunci lokaci zuwa lokaci, rabon da a aiwatar da wannan hukunci tun a 1991 a lokacin da aka kashe wani mutum wanda ya shahara wurin kashe mutane.

Ƙarancin tasiri a yanar gizo

A wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, lauyansa Oussama Bouthelja ya ce wanda yake karewa yana tsare tun watan Janairun 2024 kafin a fara shari’a.

Ya ce mahaifin yara uku ne, kuma yana aiki ne kawai a matsayin ɗan ƙwadago lokaci-lokaci, yana fama da nakasa ta dindindin da ya samu sakamakon hatsarin da ya faru da shi a wurin aikin.

Bouthelja ya bayyana shi a matsayin wanda ba shi da ilimi sosai kuma ba shi da tasiri sosai a yanar gizo.

“Yawancin abubuwan da ya wallafa ya kwafe su ne daga wasu shafuka, kuma wasu daga cikin wallafe-wallafen ba su samu wani martani ba kwata-kwata,” in ji Bouthelja.

“A kotu, ya ce niyyarsa ita ce jawo hankalin hukumomi kan mawuyacin halin rayuwarsa, ba wai tayar da tarzoma ba.”

Wannan hukuncin shi ne na baya-bayan nan da aka yi amfani da Decree 54, wata doka da ta haramta “ƙirƙira, yadawa, watsawa ko rubuta labaran ƙarya ... da nufin keta haƙƙin wasu, cutar da tsaron jama’a ko tsaron ƙasa, ko kuma cusa fargaba a tsakanin al’umma.”