AFIRKA
2 minti karatu
RSF ta kai hari da jirgi maras matuƙi na ƙunar baƙin-wake kan fararen-hula a Sudan – Sojoji
Rundunar Sojin Sudan ta zargi ƙungiyar RSF da kai hari kan fararen-hula a Kordofan ta Arewa da ke kudancin Sudan ta hanyar amfani da jirgi maras matuƙi.
RSF ta kai hari da jirgi maras matuƙi na ƙunar baƙin-wake kan fararen-hula a Sudan – Sojoji
Ba a samu rahoton asarar rayuka daga harin ba / AP
17 awanni baya

Rundunar Sojin Sudan ta zargi dakarun Rapid Support Forces (RSF) a ranar Lahadi da kai hare-haren jirgi maras matuƙi kan wuraren fararen-hula a jihar Kordofan ta Arewa da ke kudancin Sudan.

A cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun bayyana cewa dakarun RSF sun kai hari kan wasu wuraren fararen hula a birnin El-Obeid, babban birnin jihar, ta hanyar amfani da jiragi maras matuƙi na ƙunar baƙin-wake, inda suka lalata Asibitin Al-Dhaman, wasu unguwannin jama’a da wasu gine-gine a ranar Asabar da dare.

Ba a samu rahoton asarar rayuka daga harin ba

Sojojin Sudan sun bayyana harin da RSF ta kai a matsayin wata alama da ke nuna yadda kungiyar ta ‘yan tawaye ke ci gaba da karya dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa tare da cutar da fararen hula marasa laifi.

Sojojin sun ƙara ƙwace iko

Babu wani martani kai tsaye daga RSF kan wannan sanarwa ta sojojin.

Hari na baya-bayan nan ya zo ne a daidai lokacin da yankunan da RSF ke riƙe da su ke kara raguwa cikin sauri a makonnin da suka gabata, yayin da sojojin ke ƙara ƙarfin iko a jihohin Khartoum, White Nile, da Kordofan ta Arewa.

A halin yanzu, kasancewar RSF ta taƙaita ne kawai a wasu yankuna na Kordofan ta Yamma, Kordofan ta Kudu, da jihohin Blue Nile, tare da wasu sassan jihohi hudu daga cikin biyar na Darfur.

Tun daga tsakiyar watan Afrilu na shekarar 2023, sojojin Sudan da RSF ke fafatawa a wani yaƙi da har yanzu an kasa yin sulhu duk da mawuyacin halin jin kai da ƙasar ke ciki.