AFIRKA
2 minti karatu
'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 14 a sansanin ‘yan gudun hijira na DR Kongo
Harin da aka kai a yankin Djugu ya afku ne a ranar Alhamis a daidai lokacin da mutanen da suka rasa matsugunansu daga yankin Rhoo ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu a ƙauyukan da ke kewaye, a cewar rahoton.
'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 14 a sansanin ‘yan gudun hijira na DR Kongo
Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin. / Others
3 Oktoba 2025

Aƙalla mutane 14 ne aka kashe a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira a lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, kamar yadda kafafen yada labarai na ƙasar suka bayyana.

Harin da aka kai a yankin Djugu ya afku ne a ranar Alhamis a daidai lokacin da mutanen da suka rasa matsugunansu daga yankin Rhoo ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu a ƙauyukan da ke kewaye, a cewar rahoton.

Gidan rediyon Majalisar Ɗinkin Duniya, ya shaida wa manema labarai cewa, waɗanda harin ya rutsa da su manoma ne, ya kuma danganta harin da ƙungiyar ‘yan tawayen Cooperative for Development of Congo (CODECO).

“Shaidu sun ruwaito cewa ‘yan tawayen sun yi wa manoman kwanton ɓauna ne, kana suka buɗe wuta tare da jikkata wasu ta hanyar yankar su da wuƙaƙe, akwai yiwuwar adadin ya zarce haka saboda ba tsoron iya shiga yankin,” in ji rahoton.

Fargaba a sansanin

Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin.

Bayan harin, fargaba ta mamaye yankin na Rhoo, wanda ke ɗauke da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu, a cewar rahoton.

Shugabannin ƙungiyoyin fararen-hula na yankin sun yi kira ga sojoji su gaggauta shiga tsakani domin tabbatar da tsaron yankin.

Ƙasar Kongo dai ta fuskanci ɗaya daga cikin rikice-rikice mafi daɗewa da aka ganin inda mutane miliyan 7 suka rasa matsugunansu a ƙasar, a cewar MDD.

Ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai suna yawan kai hari kan fararen hula a gabashin Kongo.

A watan Yuli kadai Majalisar Dinkin Duniya ta tattara munanan hare-haren ƙungiyar Allied Democratic Forces (ADF), da na CODECO da kuma na mayakan sa kai na Raia Mutomboki/Wazalendo a Ituri, da Kivu ta Kudu da kuma Arewacin Kivu.