AFIRKA
2 minti karatu
Hare-haren RSF sun kashe gomman mutane a yankin Darfur na Sudan: Likitoci
Cibiyar Likitocin Sudan (Sudan Doctors Network) ta ce cikin waɗanda suka jikkata akwai yara bakwai da mace mai juna biyu, a harin da aka kai unguwannin zama na Al Fasher, babban birnin Arewacin Darfur da ke yammacin Sudan.
Hare-haren RSF sun kashe gomman mutane a yankin Darfur na Sudan: Likitoci
Tun daga tsakiyar watan Afrilun 2023, rikici tsakanin Sojojin Sudan da dakarun RSF ya kashe mutane fiye da mutum 20,000. / AA
6 Oktoba 2025

Aƙalla fararen hula 13 aka kashe, wasu 19 kuma suka jikkata a harin bam da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kai a Arewacin Darfur, in ji likitocin yankin a ranar Litinin.

Cibiyar Likitocin Sudan (Sudan Doctors Network) ta ce cikin waɗanda suka jikkata akwai yara bakwai da mace mai juna biyu, a harin da aka kai unguwannin zama na Al Fasher, babban birnin Arewacin Darfur da ke yammacin Sudan.

Kungiyar ta ce akwai fararen hula da dama da suka maƙale a yayin da ake ci gaba da kai hari a yankin.

Ta yi Allah wadai da harin RSF a matsayin “laifin yaƙi cikakke da kuma kai tsaye a kan rayukan fararen hula, a daidai lokacin da ƙasashen duniya suka yi shiru da nuna gazawarsu wurin kare dubban mazauna da suka makale a cikin birnin.”

20,000 sun mutu, miliyan 15 sun rasa muhallansu

Kungiyar ta roƙi al’ummar duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya su ɗauki mataki nan take don dakatar da hare-hare kan fararen hula, tare da samar da kariya ta inganci ga jama’a da ma’aikatan lafiya.

RSF ta ƙaƙaba wa birnin Al Fasher takunkumi tun daga ranar 10 ga Mayun 2024, duk da gargaɗin ƙasashen duniya game da hatsarin da ke tattare da birnin, wanda ke zama cibiyar ayyukan agaji ga jihohi biyar na Darfur.

Tun daga tsakiyar watan Afrilun 2023, rikicin da ya barke tsakanin sojojin Sudan da RSF ya kashe fiye da mutane 20,000, yayin da kimanin mutane miliyan 15 suka rasa matsugunansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin cikin gida. Wani bincike daga jami’o’in Amurka kuma ya kiyasta adadin mutanen da suka mutu ya kai kusan 130,000.