Hukumomin Afirka Ta Kudu sun bai wa Falasɗinawa ‘yan gudun hijira 153 izinin shiga ƙasar a ranar Alhamis a cikin wani jirgi daga Kenya, bayan da suka nemi mafaka a ƙasar, amma da farko an hana su shiga bayan sun fuskanci matsala a gwaje-gwaje.
Hukumar kula da bakin iyakar ƙasar (BMA) ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa a lokacin intabiyu, Falasɗinawan ba su bayyana adadin ranakun da za su yi a ƙasar ba da kuma adireshin inda za su zauna.
“Fasinjojin kuma ba su da hatimin ficewa kan fasfo ɗinsu,” in ji kwamishinan BMA Michael Masiapato.
‘Yan gudun hijirar Falasɗinawan sun shafe fiye da sa’o’i 10 a kan titin jirgi na filin jiragen saman OR Tambo kusa da birnin Johannesburg suna jiran a ba su izinin shiga ko kuma a mayar da su.
Labarin ya janyo ɓacin rai tsakanin masu fafatuka a ƙasar da aka fi sani da goyon bayan ‘yancin Falasɗinawa.
Afirka ta Kudu ta gabatar da ƙara a kotun hukunta manyan laifuka ta (ICJ) a Hague ranar 29 ga watan Disamba na shekarar 2023, inda ta zargi Isra’ila, wadda take kai hare-hare Gaza tun watan Oktoban 2023, da gaza martaba yarjejeniyar da ta shiga ta hana kisan ƙare dangi ta shekarar 1948.
Asalin makoma
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta kuma bayyana a lokuta da dama cewa tana tare da Falasɗinawa.
Sai dai kuma hukumar BMA, ta ce ta samu wasiƙa daga ƙungiyar jinƙai ta Gift of the Givers Foundation wadda ta ce za ta bai wa matafiyan wurin zama a ƙasar.
Masiapato ya ce Falasɗinawan suna da izinin zama ƙasar na kwanaki 90 ba tare da buƙatar biza ba, kuma an ba su izinin shiga kamar yadda ake yi tare da buƙatar cewa su mutunta dukkan sharuɗan shigarsu ƙasar.
“Kawo lokacin ba su iznin shiga, 23 daga cikin 153 (Falasɗinawa) sun riga sun sauya wuri (ƙaura) daga Afirka Ta Kudu zuwa asalin inda suke zon zuwa,” a cewar BMA, tana mai cewa sauran mutum 130 ɗin sun kasance a cikin ƙasar a ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Gift of the Givers Foundation.
Imtiaz Sooliman, shugaban ƙungiyar Gift of the Givers Foundation, ya bayyana a wata sanarwa cewa Isra’ila ba ta bai wa Falasɗinawan hatimin ficewa a fasfo ɗinsu ba a lokacin da suka fice.
Kwanciyar hankali
“Da gangan Isra’ila ta ƙi buga hatimi kan fasfo ɗin waɗannan mutanen (domin) ta’azzara wahalarsu a wata ƙasar waje,” in ji shi.
Falasɗinawan sun bayyana kwanciyar hankalinsu bayan an basu izinin sauka daga jirginsu. ‘Yan uwa da abokanai da ƙungiyoyin da ke kishin Falasɗinawa ne suka yi maraba da su.
“Ina godiya da kasancewa a nan. Na ɗauka ba za su bari mu shiga ba ne. Yanzu zan iya zuwa Alƙahira domin in haɗu da iyalina a can,” kamar yadda wata ɗaliba ‘yar Falasɗinu ta bayyana wa manema labarai.
Ta ce tana fatan ci gaba da karatunta a Masar.
Sooliman ya gode wa Ministan Harkokin Wajen Afirka Ta Kudu Ronald Lamola da Zane Dangor, babban darakatan hukumar hulɗa da ƙasashen wajen na Afirka Ta Kudu (DIRCO), domin ceton da suka yi wa ‘yan gudun hijirar Falasɗinu da suka maƙale.
Ya ce Lamola ne ya yanke shawarar rubuta wasiƙa zuwa ga Ma’aikatar Cikin Gida, wadda ta ɗauke musu sharaɗin hatimin fita domin bai wa Falasɗinawan damar shiga ƙasar.
Jirgin shi ne na biyu da ya ɗauki Falasɗinawa da ke tserewa daga kisan ƙare dangi a Gaza zuwa Afirka Ta Kudu.
Jirgi na farkon ya sauka ne a watan da ya gabata a filin jiragen sama na OR Tambo ɗauke da Falasɗinawa 176.

















