Ofishin kare haƙƙin ɗan’adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta ta Nuwamba 2024 da Isra'ila ta yi a Lebanon ya haifar da mutuwar fararen-hula 114.
Mai magana da yawun ofishin, Thameen Al-Kheetan, ya bayyana wa Anadolu cewa ofishin na bibiyar farmakin jiragen sama na Isra'ila a kan gine-gine a ƙauyukan da ke kudu, ya kuma ce mutuwar fararen-hula ta ci gaba da ƙaruwa tun lokacin da aka tsagaita wuta.
Ya jaddada cewa dole ne a dakatar da kisan da ake ci gaba da yi wa fararen-hula "nan take", yana mai cewa mazauna yankin sun yi rayuwa cikin rashin tabbas da fargaba fiye da shekaru biyu.
Haka kuma ya yi kira da a gaggauta bin yarjejeniyar dakatar da tashin hankali da kuma dokokin jinƙai na kasa da kasa.
Sojojin Isra'ila sun kashe fiye da mutum 4,000 kuma sun jikkata kusan 17,000 a hare-harensu kan Lebanon, wanda suka fara kaiwa tun Oktoban 2023 inda zuwa Satumban 2024 hare-haren suka ƙazanta.

















