Dakarun ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinu Hamas sun kashe mutum 32 daga cikin wani “gungu” a birnin Gaza a wani yunƙurin tsaro da aka fara bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar Jumma’a.
Mutane shida daga cikin ‘yan ƙungiyar ta Hamas su ma sun rasa rayukansu a rikicin, kamar yadda wata majiyar tsaro ta Falasɗinu ta shaida wa Reuters a ranar Litinin.
Jami’in ya bayyana cewa aikin tsaron da aka gudanar a birnin Gaza an yi shi ne da nufin daƙile ayyukan mambobin wata “ƙungiya mai haɗari da ke da alaƙa da wani iyali a birnin Gaza”.
Wannan aiki ya kai ga kama mutum 24 tare da raunata wasu 30, in ji jami’in.
A baya, an ruwaito cewa Isra’ila ta tallafa wa wata ƙungiya mai ɗauke da makamai a Gaza da nufin raunana ikon Hamas a yankin na Falasɗinu. Ƙungiyar tana da hannu a wajen satar kayan agaji.
Tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Isra’ila a Gaza da ya shafe shekaru biyu ta fara aiki, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza ta tura jami’an tsaro domin cike wani giɓi na tsaro da zai iya haifar da rashin doka da oda da kuma sata.
Yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci Hamas ta ajiye makamai a wani shiri na kawo ƙarshen yakin Gaza, ya ba da dama ga Hamas ta gudanar da ayyukan tsaro na cikin gida, yana mai cewa suna son “dakatar da matsalolin” kuma “mun ba su izini zuwa wani lokaci.”
Hamas ta taɓa zargin Yasser Abu Shabab, shugaban wata ƙungiya, da magoya bayansa da yin haɗin baki da Isra’ila.
Jami’in tsaron na Hamas ya ce an “kashe” wani babban mataimaki na Abu Shabab tun bayan da aka fara wannan aikin tsaro tare bayan tsagaita wuta, kuma ya ce ana ci gaba da neman Abu Shabab.
“Aikin tsaron yana ci gaba kuma yana faɗaɗa har sai an gama shi gaba ɗaya, kuma ba za a bari kowace ƙungiya ta karya doka ba,” in ji shi.