Za a iya samun dawwamammen zaman lafiya a Gaza ne kawai ta hanyar samar da kasashe biyu, Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shaida wa Firaministan Birtaniya Keir Starmer, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin yin hakan.
Taron wanda ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata yayin ziyarar da Erdogan ya kai birnin Sharm el-Sheikh na kasar Masar, domin halartar taron kasa da kasa kan shirin samar da zaman lafiya a Gaza, ya tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma batutuwan da suka shafi yankin da na duniya baki daya, in ji Hukumar Sadarwa na Turkiyya a shafin sadarwa na yanar gizo na Turkiyya NSosyal.
Ankara ta yi aiki tukuru wajen kawo karshen hare-haren Isra'ila tare da cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, shugaban na Turkiyya ya fada wa Firaministan Birtaniya, yana mai jaddada cewa kokarin da ake na ganin an tsagaita wuta da share fagen samar da zaman lafiya zai ci gaba da karu wa.
Erdogan ya kuma jaddada bukatar agajin jin kai ba tare da tsaiko ba don isa Gaza da kuma fara aikin sake gina yankin cikin gaggawa.
Ya ce suna kokarin inganta hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Birtaniya a dukkan fannoni, musamman ma a fannin tsaro.
Ganawar Erdogan da mataimakin shugaban kasar UAE
Erdogan ya kuma gana da mataimakin shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kuma mataimakin Firaministan kasar Sheikh Mansour bin Zayed Al Nahyan.
A yayin ganawar, shugabannin biyu sun tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yankin da duniya baki daya, kamar yadda wata sanarwa da Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta fitar.
Shugaba Erdogan ya jaddada cewa, karfafa alakar siyasa a tsakanin Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ya taimaka matuka wajen hadin gwiwa a fannin kasuwanci da zuba jari.
Ya ce dukkanin bangarorin biyu suna kokarin habaka hadin gwiwa a sauran fannoni, musamman ma fannin tsaro.
A yayin da yake magana kan halin da ake ciki a Gaza, Shugaba Erdogan ya ce, Turkiyya na kokarin kawo karshen kisan kiyashin da ake yi, kuma an fara bude kofofin damarmaki don samar da zaman lafiya mai dore wa — wanda dole ne a yi amfani da su sannu a sannu.
Ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita wutar, da tabbatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza ba tare da samun tsaiko ba, da kuma kaddamar da ayyukan sake gina yankin nan take.
An fara sakin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila a ranar Litinin din nan bayan da kungiyar Hamas ta sako daukacin ‘yan Isra’ila 20 da aka yi garkuwa da su a Gaza a wani bangare na yarjejeniyar da aka cim ma a makon jiya na kawo karshen yakin da ake yi a yankin Falasdinu.
Kazalika, Erdogan ya kuma yi ganawar sirri da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron, da Firaministar Italiya Giorgia Meloni, da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.