Gwamnatin Nijeriya ta umarci jami’an tsaron kasar su kubutar da ‘yan matan da wasu ‘yan bindiga suka sace a jihar Kebbi a farkon makon nan.
Ministan Watsa Labarai na kasar Mohammed Idris ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shainsa na X ranar Litinin.
“An umarci jami’an tsaronmu da jami’an leken asiri su gano, tare da kubutar da daliban da kuma dawo da su cikin aminci,” a cewar minitstan.
Ya kara da cewa, “Gwamnatin Tarayya ba za ta saurara ba har sai an cim ma wannan buri.”
A cikin daren Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suke kai hari a Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar, suka kuma tafi da dalibai mata 25, a cewar runduna ‘yan sandan jihar Kebbi.
Rundunar ta ce bayan faruwar lamarin, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Bello Muhammad Sani, ya tura jami’an ‘yan sanda na musamman tare da jami’an soji da ƙungiyoyin ‘yan bijilanti zuwa yankin.
A sanar da ministan watsa labaran ya fitar, ya ce, gwamnatin tarayya ta damu sosai da faruwar lamarin, sannan tana tare da iyalan wadanda abin ya shafa.
Mohammed Idris ya ce gwamnati na sauya fasallin sojojin kasar, da ‘yan sanda da hukumomin leken asiri, ta yadda za su iya hana sake aukuwar irin wadannan hare-hare, tare da mayar da martani cikin gaggawa a duk lokacin da aka samu matsala irin wannan.
Ya kara da cewa Nijeriya tana jaddada hadakarta da kawayenta a yankin, ta hanyar ECOWAS, da Kungiyar Tarayyar Afirka da Dakarun Hadin Gwiwa na Kasa da Kasa, “don tsare kan iyakokinmu da kuma hana kungiyoyin masu aikita laifuka walwala.”
















