Yadda ta kaya a zaman 'yan majalisar Amurka kan zargin yi wa Kirisotci kisan kiyashi a Nijeriya
NIJERIYA
5 minti karatu
Yadda ta kaya a zaman 'yan majalisar Amurka kan zargin yi wa Kirisotci kisan kiyashi a NijeriyaAn shafe lokaci ana lugudan laɓɓa da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran waɗanda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet.
US Congress
21 Nuwamba 2025

Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan batun na Nijeriya.

Zaman, wanda aka yi a Majalisar Dokokin Amurka da ke birnin Washington a ranar Alhamis ya ƙunshi ’yan majalisa da masu kare hakkin dan’adam da kuma wasu kungiyoyin fararen hula.

An shafe lokaci ana lugudan laɓɓa da musayar yawu tsakanin mambobin majalisar da sauran waɗanda suka halarci zaman, wanda aka kuma yada shi kai-tsaye ta intanet.

Masu magana a wajen sun haɗa da Babban Jami’i na Cibiyar Harkokin Amurka Jonathan Pratt da Mataimakin Sakataren Cibiyar Dimokuradiyya, Hakkokin Dan’adam da Ƙwadago, Jacob McGee.

Sa kuma Daraktar Cibiyar ‘Yancin Addini, Ms Nina Shea; da Bishop Wilfred Anagbe na Cocin Katolika ta Makurdin Nijeriya; da Ms Oge Onubogu ta Cibiyar Dabaru da Karatun Ilimin Ƙasa da Ƙasa, waɗanda suka sha tambayoyi daga ‘yan majalisar.

Yayin da wasu mambobin suka goyi bayan ayyana Nijeriya a matsayin “kasar da Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini” da daukar mataki kan Nijeriya lokacin da suke jawabi, akwai wasu daga cikin mambobin majalisar da suka bukaci a sake duba matsayin da Amurkan ta ɗauka, inda suka ce abubuwan da ke faruwa suna da sarƙaƙiya kuma suna bukatar a duba su da idon basira.

Ko da yake Shugaban Kwamitin, Chris Smith wanda ɗan jam’iyya mai mulki ta Republican ne kuma yana wakiltar Jihar New Jersey, yayin da yake jawabin bude taron ya bayyana cewa zaman yana da muhimmancin gaske, don Amurka ba za ta zuba ido kan abubuwan da suke faruwa a Nijeriya ba, kuma hakan ne ya sa yake yawan kira kan cewa akwai bukatar a dauki mataki kan ƙasar.

Sai dai wasu ’yan majalisar dokokin Amurka ba su goyi bayan matsayin Shugaba Trump kan cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya ba.

’Yar majalisar wakilai ’yar jam’iyyar adawa ta Democrat Pramila Jayapal ta ce ba ta goyon bayan daukar matakin soji a kan Nijeriya, inda ta bayyana cewa Nijeriya tana da matukar muhimmanci ga Amurka da ƙasashen Afirka.

Ta ce kashe-kashen da ke faruwa a Nijeriya ba Kiristoci kawai yake shafa ba, inda ta ce ana kashe hatta mabiya sauran addinai a kasar.

Sannan ’yar majalisar ta mayar wa Shugaba Trump martani inda ta ce kuskure ne a yi wa wata ƙasa barazana a kafar sada zumunta ta Truth Social kuma barazanar ma har da ta amfani da ƙarfin soja a kanta.

Ita ma ’yar majalisar wakilai daga Jam’iyyar Democrat Sara Jacobs ta nuna rashin goyon bayanta kan matayin da Shugaba Trump ya dauka a kan Nijeriya, inda ta ce ba gaskiya ba ne a ce Kiristoci kadai ake kashewa a ƙasar.

’Yar majalisar wacce ta taɓa yin aiki a Nijeriya a karkashin wani shirin yaƙi da ta’addanci na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a shekarar 2013, ta ce kashe-kashen da ke faruwa a Nijeriya yana shafar duka Musulmai da Kiristoci, kuma ta ce akwai bukatar gwamnatin Nijeriyar ta yi wani abu a kan hakan.

Sannan ta bayar da misalai biyu da suka faru a baya bayan nan, na kashe wasu Kiristoci biyu a coci da aka yi Jihar Kwara, da kuma na yadda aka sace dalibai mata 25 a Jihar Kebbi waɗanda dukkansu Musulmai ne, inda ta ce hakan manuniya ce kan cewa tashin hankalin yana shafar kowa da kowa.

Kazalika wani babban jami’i kuma darakta a Cibiyar Shirin Afirka da Dabaru da Karatun Ilimin Ƙasa da Ƙasa, Oge Onubogu, ta gargadi Amurkan kan amfani da ƙarfin soja a Nijeriya, tana mai cewa yin hakan zai sanya su kansu Kirisotocin da ake son bai wa kariya cikin hatsari.

Akwai kuma wata tambaya da aka yi wa wani babban jami’i na sashen Cibiyar Harkokin Afirka na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Amurka, Jonathan Pratt kan ko akwai ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke kutsa kai cikin gwamnatin Nijeriya?

Sai ya ce, "Bai yarda cewa masu tsaurin ra’ayi sun kutsa kai cikin gwamnatin Nijeriyar ba."

Tambaya ta ƙarshe da ‘yar majalisa Sarah Jacobs ta yi kan ko yaya gwamnatin Nijeriya ta ɗauki batun Trump kan saka wa ƙasar ido na musamman kan walwalar addini, ita ta nuna cewa a yanzu ana kan matakin tattaunawa ne tsakanin ƙasashen biyu.

Pratt ya amsa mata da cewa gwamnatin Nijeirya ta ɗauki batun da muhimmanci sosai, yana mai cewa tuni manyan wakilan Nijeriya suka je Amurka, kuma za su gana da manyan jami'an gwamnatin Amurka a wannan makon.

Sannan ya ce sun riga sun dauki matakai tsakanin gwamnati a Abuja da kuma a Washington kan shirin aiwatarwa, yana mai cewa sakamakon da ake samu a yanzu dangane da hain gwiwar Nijeriya da Amurka kan wannan batu sakamako ne mai kyau.

Rumbun Labarai
Jerin lokutan da aka shafe ana shari'ar Nnamdi Kanu, jagoran 'yan a-waren Biafra a Nijeriya
‘Yan bindiga sun sace ɗalibai da ma’aikata a wata makaranta a Jihar Neja
Jagoran ƴan-awaren Biafra: Babbar Kotu a Nijeriya ta yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai
'Yan Nijeriya miliyan 45 suna bahaya har yanzu a waje — Ministan Muhalli
Ribadu ya jagoranci wata tawagar Nijeriya mai ƙarfi zuwa Amurka kan zargin kashe Kiristoci a ƙasar
Kotu ta yanke wa wani shugaban ISWAP da ya tsara hare-haren kano na 2012 ɗaurin shekara 20
Tinubu ya ɗaga tafiyarsa tarukan G20 da AU-EU saboda yanayin rashin tsaro da ake ciki a Nijeriya
Majalisar Dattawan Nijeriya ta nemi a ɗauki ƙarin sojoji 100,000 don magance rashin tsaro
Tinubu ya yi alhinin mutuwar Janar Uba da 'yan ta'adda suka kashe a Borno
Majalisar Dokokin Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis
Gwamnatin Jihar Katsina za ta shirya muƙabala tsakanin Yahya Masussuka da sauran Malaman Musulunci
Babban hafsan sojin Nijeriya ya je Jihar Kebbi ya nemi  a tsaurara neman 'yan matan da aka sace
Gwamnatin Nijeriya ta umarci jami’an tsaro su kuɓutar da ɗalibai mata da aka sace a Jihar Kebbi
Nijeriya tana tattaunawa kan tsaro da Amurka bayan barazanar Trump: Yusuf Tuggar
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da tallafin jarin N50m ga ɗalibai a fannin ƙirƙire-ƙirƙire
Rikicin PDP: Ɓangaren Wike ya yi watsi da kora yayin da jihohi huɗu ke ƙalubalantar Makinde
‘Yan sandan Nijeriya sun tabbatar da sace ɗalibai ‘yan mata 25 a Kebbi
Sojojin Nijeriya sun daƙile kwanton-ɓauna, sun yi watsi da jita-jitar sace wani janar na soja
Kasafin kuɗin gwamnatin kano na 2026 zai haura naira tiriliyan ɗaya - Gwamna Abba Kabir
Yaya karawar Nijeriya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo za ta kasance?