Wata kotun tarayyar Nijeriya a Abuja ta yi wa wani shugaban ƙungiyar ta’addancin ISWAP, Hussaini Ismaila, ɗaurin shekara 20 bisa laifukan ta’addanci.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba bayan samun Ismaila da aka fi sani da Mai Tangaran da laifukan shirya hare-haren ta’addanci a Kano ranar 20 ga Janairun 2021, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 150.
Da farko, Mai Tangaran ya musa tuhumue-tuhumen da Hukumar Tsaron Farin kaya ta DSS ta gabatar a kansa, amma daga baya ya amsa laifinsa bayan gabatar da shaidu.
Kotun ta yi wa Ismaila ɗaurin shekara 15 a kan tuhuma ta ɗaya, kuma an yi masa ɗaurin shekara 20 a kan tuhuma ta biyu da ta uku da ta huɗu, kuma zai yi zaman kason dukkan ɗaurin ne a lokaci guda, tun daga ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2017, lokacin da DSS ta kama shi.
Alƙalin ya kuma ba da umarni ga shugabna Hukumar Gidajen Yari ta Nijeriya da ya tsare mutumin cikin ko wane gidan yarin da ya ga dama, har sai lokacin da ya ƙarasa zaman kasonsa, yana mai ƙarawa da cewa dole a saka a saka shi a shirin gyaran hali da kuma kawar da tsatssauran ra’ayi bayan ya gama zaman kaso kafin ya koma cikin al’umma.
Masu gabatar da ƙara sun ce Ismaila ne ya jagoranci hare-haren da aka kai a shekarar 2012 kan hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Bompai, jihar Kano da ofishin shiyya ta daya ta rundunar ‘yan sandan Nijeriya a jihar Kano da ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Farm Centre da na Ungwa Uku, duka a jihar Kano, inda aka kashe mutane fiye da 150, wasu daruruwa kuma suka ji rauni.
Jinkirin Shar’ia
Jim kaɗan bayan kama shi a ƙauyen Tsamiyya Babba da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano a shekarar 2017, an gurfanar da Ismaila a gaban kuliya inda aka tuhume shi da laifuka ƙarƙashin dokar hana ta’addanci ta shekarar 2013.
Shari’arsa ta fuskanci jinkiri daga ɗaukaka ƙara da kuma yin shari’a cikin shari’a, domin tabbatar da gaskiyar cewa wanda ake tuhumar ya yi bayanai ne bisa radin kansa ba bisa tursasawa ba.
A lokacin da aka ci gaba da shari’ar daga baya kuma, masu gabatar da ƙara sun gabatar shaidu biyar, ciki har da jami’an DSS biyu da kuma shaidun gani da ido da suka shaida wasu daga cikin hare-haren.
Ismaila, wanda ya musanta zargin da farko, ya sauya ra’ayi inda ya amsa lafukan bayan kammala gabatar da shaidu.
Daga baya, lauyan wanda ake tuhuman, P. B. daga ƙungiyar lauyoyi masu taimaka wa mutane wato Legal Aid Council (LAC), ya roƙi kotun da ta yi wa mutumin sassauci.
Onijah ya ce Ismaila ya yi nadama kuma ya sauya abin da ya gaya wa kotu domin kada ya ɓata mata lokaci, kuma ya yi nadamar kasancewa da hannu a cikin ta’addanci.
















