Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya (COAS), Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun soji a karkashin rundunar Operation FANSAN YANMA da su kara himma wajen ceto daliban da aka sace daga Makarantar Sakandare ta 'Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) a karamar Hukumar Danko/Wasagu ta Jihar Kebbi.
Janar Waidi Shuaibu ya bayar da umarnin ne a ranar Litinin, 17 ga Nuwamban 2025, yayin ziyarar aiki da ya kai Jihar ta Kebbi, kwana guda bayan harin da ’yan bindiga suka kai makarantar.
Da yake jawabi ga kwamandoji da sojoji da ke fagen daga, COAS ya bukace su da su kara himma wajen gudanar da ayyukan leken asiri tare da bin diddigin ‘yan bindigar da suka sace daliban.
"Dole ne mu nemo waɗannan yaran. Ku yi aiki cikin hikima da ƙwarewa kan duk wasu bayanan sirri,” in ji Janar Shaibu, yana mai cewa “Babu wani zaɓi a batun yin nasara.”
A wani ɓangare na ziyarar, Janar Shaibu ya kuma gana da 'yan banga da mafarauta na yankin, yana mai bayyana su a matsayin muhimman abokan aiki a wannan lokaci na aikin da ake gudanarwa.
Ya karfafa musu gwiwa da su yi aiki kafada da kafada da sojoji tare da amfani da iliminsu na ƙasa don taimakawa wajen gano masu laifin.
"Tare za mu maido da zaman lafiya da kuma tabbatar da cewa 'ya'yanmu za su iya zuwa makaranta ba tare da tsoro ba," a cewar Babban Hafsan Sojin.
















