Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace dalibai ashirin da biyar daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe a lokacin da ƴan bindiga suka mamaye makarantar, inda suka kashe wani ma’aikaci ɗaya tare da jikkata wani.
A cewar wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan, CSP Nafi’u Abubakar Kotarkoshi ya sanya wa hannu, maharan ɗauke da makamai masu ƙarfi sun kutsa makarantar inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro da ke bakin aiki. Duk da ƙoƙarin jami’an, an ruwaito cewa maharan sun haye katangar makarantar suka kuma yi awon gaba da ɗaliban daga ɗakunan kwanan su.
Jami’in ya tabbatar da cewa Hassan Makuku wanda rahotanni suka ce shi ne mataimakin shugaban makarantar ya rasa ransa yayin harin, yayin da wani Ali Shehu ya samu rauni sakamakon harbinsa da bindiga a hannunsa na dama.
Bayan faruwar lamarin, sanarwar ta ce Kwamishinan ‘Yan Sanda, Bello Muhammad Sani, ya tura jami’an ‘yan sanda na musamman tare da jami’an soji da ƙungiyoyin ‘yan bijilanti zuwa yankin.
Tawagar haɗin gwiwa na ci gaba da bincike a hanyoyin da ake zargin maharan sun bi da dazuzzukan da ke kewaye domin gudanar da aikin ceto da kuma kama waɗanda suka aikata laifin.
Kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da muhallinsu, yana tabbatar musu da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.
















