Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ɗage tafiyar da aka shirya zai yi zuwa birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu da Luanda da kuma Angola, saboda zai karɓi ƙarin bayanai na tsaro kan ‘yan mata ‘yan makaranta da aka sace a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai Cocin Christ Apostolic a Eruku da ke Jihar Kwara.
Wata sanarwa da Mai Taimaka wa Shugaban Kasa na Musamman kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba ta ce, “A bisa buƙatar gwamnan Jihar Kwara, Shugaba Tinubu ya ba da umarnin aika ƙarin dakaru zuwa Eruku da ma baki ɗayan ƙaramar hukumar Ekiti da jihar.
“Ya kuma umarci ‘yan sanda da su yi farautar ‘yan bindigar da suka kai wa masu ibada hari,” in ji sanarwar.
A ranar Talata da yamma ne ‘yan bindiga suka kai hari kan wani coci a garin Eruku na Jihar Kwara, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da sace wasu da dama.
Rahotanni sun ce wasu mutane ɗauke da makamai, sun shiga Cocin Christ Apostolic da ke Oke Isegun a ƙaramar hukumar Ekiti a lokacin da ake tsaka da ibadar yamma, suka harbe limamin cocin kuma suka tasa ƙeyar masu ibadar da yawa.
Tun da fari an tsara cewa Shugaba Tinubu zai bar Abuja a ranar Laraba don halartar Taron G20 karo na 20 a Afirka ta Kudu, inda daga can zai wuce Luanda don halartar taron Ƙungiyar Hadin Kan Afirka da na Tarayyar Turai wato AU-EU.
“Amma saboda damuwar da ya shiga bayan harin da aka kai Jihar Kebbi da wanda ‘yan bindiga suka kai a kan masu ibada a Cocin Christ Apostolic da ke Eruku, Shugaba Tinubu ya yanke shawarar dakatar da tafiyarsa.
“A yanzuyana jiran rahoto daga Mataimakin Shugaban KAsa Kashim Shettima, wanda ya kai ziyarar jaje zuwa Kebbi a madadanis, tare da jiran rahoto daga ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya kan harin na Kwara.”
A ƙarshe Shugaba Tinubu ya jaddada umarninsa ga hukumomin tsaro cewa su yi duk mai yiwuwa don ceto ‘yan maran sakandaren nan 24 waɗanda ‘yan bindiga suka sace, tare da mayar da su gida cikin aminci.
Harin Coci na Kwara
Tuni ‘yan sanda suka ce sun gano gawar mutum na biyu a cikin wani daji, kazalika wani jami'in sa-kai ya jikkata sakamakon harbin sa da aka yi, kuma tuni aka kai shi asibiti.
Hukumomi a jihar sun ce ‘yan sanda da ‘yan sa-kai sun bazama farautar maharan waɗanda suka tsere cikin dazukan da ke kusa.
An yi ta yaɗa wani bidiyo da ake kyautata zaton na kyamarar CCTV ne na cocin a shafukan sada zumunta, wanda ke nuna masu ibadar a tsorace suna neman mafaka, ciki har da tsofaffi da ke ta ƙoƙarin guduwa.
















